Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban kasar Siriya yace za a fuskanci "girgizar kasa" idan kasashen yammaci suka yiwa kasar katsalandan


Masu zanga zangar kin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya
Masu zanga zangar kin jinin gwamnatin shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya yi gargadi cewa, za a iya fuskanci abinda ya kira “girgizar kasa” a duk fadin Gabas ta Tsakiya idan shugabannin kasashen yammaci suka yi katsalandan a harkokin kasarshi.

Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya yi gargadi cewa, za a iya fuskanci abinda ya kira “girgizar kasa” a duk fadin Gabas ta Tsakiya idan shugabannin kasashen yammaci suka yi katsalandan a harkokin kasarshi.

A cikin hirar da jaridar Birtaniya Daily Telegraph tayi da shi, Mr. Assad yace Siriya ta banbanta ta kowacce hanya da Misira, Tunisiya ko Yemen. Ya yi gargadi da cewa kasar tana iya zamewa wata “Afghanistan” idan dakarun kasashen ketare suka sa hannu da cewa, kasarshi, ita ce cibiyar Gabas ta Tsakiya, kuma duk wata matsala da aka fuskanta a kasar Siriya zata shafi yankin baki daya.

Ya bayyana haka ne ‘yan sa’oi bayanda ‘Yan gwaggwarmayar kasar suka ce an kashe a kalla sojoji da farin kaya 47 a tashe tashen hankalin da aka yi a fadin kasar jiya asabar. An yi shirin zaman tattaunawa yau lahadi a birnin Doha tsakanin gwamnatin kasar Siriya da kungiyar hadin kan Larabawa da nufin fara tattaunawa da kungiyoyin hamayya. Shugabannin adawa da dama sun bayyana zaman a matsayin bata lokaci.

Yan gwaggwarmaya sun ce a kalla mutane goma suka mutu a birnin Homs da ake fama da tashin tashina, yayinda aka kashe wadansu bakwai a wasu wurare dabam. Tashoshin talabijin sun yayata hoton bidiyon inda aka nuna dakarun dake goyon bayan shugaba Bashar al-Assad suna tada boma bamai kan birnin Homs, yankin Bab Amr, suka lalata gidaje da dama.

Kungiyar ‘yan kasar Siriya masu kare hakin bil’adama dake da zama a Birtaniya sun ce an kashe sojojin gwamnati 20 a gumurzun da wadanda ake kyautata zaton tsofaffin sojojin kasar ne da suka canza shekarar, yayinda kuma sojojin da suka canza sheka daga lardin Idlib suka yiwa wadansu jami’an tsaro goma kwantan bauna. Tashar talabijin ta Al-Arabiya ta laburta cewa, sojoji casa’in ne suka canza sheka daga rundunar sojin kasar Siriya a lardin Bab Amir ranar alhamis, abinda ya yi sanadin harin da dakarun dake goyon bayan Assad suka kai.

XS
SM
MD
LG