Majalisar dattijai ta amince ta shirin tsuke bakin aljihu d a wasu matakai da suka dauka da nufin taimakawa kasar ta fita daga cikin matsalolin tattalin arziki.
Idan majalisar wakilai ta amince da kudurin da majalisar dattijai ta maince d a shi gobe Asabar, PM Silvio Berlusconi yace zai yi murabus domin bada fili a kafa sabuwar gwamnati wadda hakan zai rarrashi masu zuba jari da kuma tarayyar turai.
Sauye sauyen dokokin kasar da aka kuduri aniya an dauka ne domin tsaida yawan bashin da ake bin gwanati kasar na dala milyan zambar biyu da dala milyan dubu dari shida.
Shugabannin tarayyar turaida masu zuba jar sun damu cewa idan ba Italiya ta dauki mataki ba, kasar wacce tattalin arzikinta shine na uku a girma a turai zai bukaci tallafi mai tsanani fiyeda abin da aka baiwa Girka, Ireland ko Portugal.
A wani lokaci a wunin yau jumma’a ake sa ran rantsar da Lucas Papademos a matsayin PM riko a da fatan zain taimakawa wajen ceto kasar daga rikicin tattalin arziki d a take fuskanta.