Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fafata Tsakanin Masu Zanga Zangar EndSARS Da 'Yan Kasuwa a Jos


Zanga Zangar EndSARS
Zanga Zangar EndSARS

Wata hatsaniya da ta tashi a titin Ahmadu Bello Way daura da Kasuwar Terminus a tsakiyar birnin Jos hedikwatar jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya tayi sanadin rasa dukiyoyi. 

Bayanai na nuni da cewa rigimar ta tashi ne bayan da wasu masu zanga-zangar #EndSARS# suka nemi kafa shinge a wata mahada da ke kasuwar da wasu muhimman sassan kasuwanci da ke kan titin Ahmadu Bello Way, sai wasu matasa da ke kasuwanci a wurin suka nuna rashin amincewarsu.

Mamba a kwamitin Tsaron kasuwar Terminus, Tijjani Bala ya ce asalin matsalar wasu masu zanga zangar nan ta #EndSARS ne suka taso suka zo kan titin Ahmadu Bello Way, inda suka fara yin jefe jefe, sai hatsaniya ta kaure a tsakaninsu da wasu matasan kasuwar.

Wanda su a matsayin su na ‘yan kwamitin tsaron kasuwa sun yi iya kokarin su na tsare dukiyoyin mutane gaba daya sai dai wanda ya fi karfinsu.

Bala ya kara da cewa kafin su isa wurin tuni wasu suka kona motoci guda hudu. Amma komai ya lafa kuma jami’an tsaro sun zo wurin don kawo dauki.

Zanga zangar EndSARS a Jos
Zanga zangar EndSARS a Jos

Shi ma wani da lamarin ya faru a gabansa, mai suna Ado Musa, ya ce banda motoci da aka kona kuma an farfasa gilasan bankuna da wasu shaguna a wurin.

Musa ya ce daga baya abin ya fara zama wani iri, ya zama wani abu daban, ba zanga zanga ba; abin ya zama ana kaiwa mutane hari da kuma kone kone.

Ita ma Amina Ahmad da abin ya ritsa da ita, ta ce an buga mata mota a lokacin da take kokarin tserewa daga wurin.

Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jahar Filato, Mr. Dan Manjang, ya ce gwamnati ta tura jami’an tsaro wurin, kuma suna iya kokarinsu domin su kwantar da wannan hatsaniyar da ta taso, saboda rigima idan ta taso ba a san yadda za ta karasa ba.

Manjang ya kuma ce wadannan matasa da suka fara wannan abun da su daina, amma duk wanda yake da hannu a ko wane bangare ya ke hukuma za ta dauki matakin da ya dace kansa.

A yanzu haka dai komai ya daidaita amma mutane na zaman dardar saboda rashin abin da zai biyo baya idan dai hukumomi ba su dauki matakin da ya da ce ba.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG