Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Sharhi Sun Kwatanta Matakan Tsaro A Washington Da Na Tarihi


Jami'an tsaro a Washington
Jami'an tsaro a Washington

Ana ci gaba da shirye shiyen mika mulki ga sabuwar gwamnati a Amurka, al’amarin da ya biyo bayan wasu batutuwa da dama, ciki har da abkawa ginin Majalisar dokokin kasar, inda har aka yi jina-jina da mace mace.

A cigaba da tabo batun na mika mulki wanda za a yi ranar Laraba, Sashen Hausa ya fara ne da tuntubar wani dan asalin Najeriya da ke jihar Maryland a nan Amurka, wanda ya lakanci siyasar Amurka, Dr Safiyanu Ali Mai Biyar, wand ya yi fashin baki a kan yanda ake gudanar da bukin.

A cewarsa wannan bukin mika mulki daga shugaban kasa mai baring ado zuwa ga zababben, buki ne da ya samo asali tun a shekarar 1937 wanda ake gudanarwa a cikin watan Janairu bayan kowane zabe da kasar ta yi a cikin watan Nuwamba.

Dr. Mai Biyar ya yaba da matakan tsaron da aka dauka saboda bukin na rantsar da shugaban kasa mai jiran gado, Joe Biden a ranar Laraba, ya kuma ce wajibi ne a dau wadannan matakan tsaro duba da irin hari da magoya bayan Trump suka kai a majalisar dokokin kasar.

Ya ce tarihi ya nuna, rabon Amurka da ganin irin wannan tarzoma a kan majalisa, tun yakin duniya na shekarar 1812, da Birtaniya ta kai hari a kan ginin majalisar saboda haushin Amurka ta 'yanta kanta daga Burtaniya din.

Dr. Mai Biyar, ya ce babu wani zaman dardar da ake yi a yankin da yake a jihar Maryland mai makwabtaka da Washington, yayin da aka tambaye shi a kan halayyan mutane a inda yake. Ya ce zababben shugaba Joe Bide ne ya lashe jihohin Virginia da Maryland masu makwabtaka da Washington DC, dan haka babu irin magoya bayan Trump masu tsatsaurar ra’ayi da yawa a wuraren.

Yayin da ‘yan Democrat ke zargin Republican da iza tarzomar ta ranar shida ga watan Janairu a majalisar dokoki, suma ‘yan Republican na zargin Democrat da ingiza tashin hankali a wasu wuraren kasar a lokacin rani, lamarin da ya haifar da cece-kuce tsakanin jam’iyyun.

Dr. Mai Biyar ya ce kisan bakar fata, George Floyd, ne ya haddasa rikicin da aka samu a lokacin ranin amma ba siyasa ba , dan haka akwai bambanci da wanda ya faru a ranar shida ga watan Janairu saboda hukumomin tsaro da dama sun tabbatar Shugaba Donald Trump ya ingiza magoya bayan sa da suka yi tawaye.

Ga dai tattaunawar Ibrahim Garba da Dr. Safiyanu Ali Mai Biyar:

XS
SM
MD
LG