Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Tsaro Sun Rufe Washington Kafin Rantsar Da Biden


Jami'in tsaro a Amurka
Jami'in tsaro a Amurka

Hukumomin tsaro kulle birnin Washington kana jami’an tsaron Amurka suna kara jan damarar tinkarar magoya bayan Trump da za su yi tattaki a manyan biranen jihohin Amurka 50 a karshen wannan mako.

Hukumomin tsaron sun kafa shingaye kana suka jibge dubban dogarawan kasa domin kare irin tarzomar da ta afkawa kasar a ranar shida ga watan Janairu.

Hukumar binciken manyan laifuka ta FBI ta gargadi hukumomin ‘yan sanda a kan yiwuwar zanga zanga da makamai a wajen gine ginen majalisun dokoki a jihohi 50 na kasar daga ranar Asabar har izuwa ranar 20 ga watan Janairu da za a rantsar zababben shugaba Joe Biden, wata tarzoma da magoya bayan Donald Trump da suka amince da kalaman sa na magudin zabe suke hurawa.

Johohi kamar Michigan, Virginia, Wisconsin, Pennsylvania da Washington suna cikin jihohin da suke amfani da dogarawan kasa wurin karfafa matakan tsaro. Itama jihar Texas ta rufe majalisar dokokinta har zuwa ranar rantsar da shugaban kasa.

Darektan ma’aikatar kare jama’a a jihar Texas, Steve McCraw ya fada da yammacin ranar Juma’a cewa bayanan sirri da suka tattara na nuni da cewa masu shirya tarzoma zasu yi amfani da zanga zanga da makamai da su shirya miyagun aiki.

A cibiyar kasuwancin Washington, jami’ai sun kama wani mutumin jihar Virginia wanda ya yi yunkurin kutsawa a shingen bincike da ‘yan sandan majalisar dokoki suka kafa a ranar Juma’a yana dauke da wasu kayayyakin bukin ranar rantsar da shugaban kasa na jabu, cike da bindigogin hannu da harsashai sama da 500, a cewar rahotannin CNN da jaridar The New York a jiya Asabar, suna nuni da wata majiyar jami’an tsaro.

An zargin mutumin da aikata laifuka guda biyar, ciki har da rike haramtattun makamai da harsashai ba bisa doka ba a cewar rahoton.

‘Yan sandan na majalisar dokokin basu ce komai ba a lokacin da aka tuntube su a kan batun.

Daukar wadannan matakan na zuwa ne bayan wani mummunar harin da magoya bayan Trump suka kai a kan majalisar dokokin Amurka a ranar shida ga watan Janairu, inda wadan su a cikin suka yi yunkurin garkuwa da wasu ‘yan majalisan kana suna kira ga mutuwar mataimakin shugaban kasa Mike Pence yayin da yake jagorantar zaman tabbatar da nasarar da Biden ya samu a zaben watan Nuwamba.

Shugabannin Democrat a kwamitocin majalisa guda hudu sun fada a jiya Asabar cewa suna sake duban abin da ya farun kana sun rubutawa hukumar binciken manyan laifuka ta FBI da wasu hukumomin liken asiri da su binciko abin da suka sani game da barazanar, ko an raba bayanai ne ko kuma akwai hannu wata kasar waje.

XS
SM
MD
LG