Dubun dubatar dakaru na shirin kwarara birnin Washington inda ake kara kewayewa da jami’an tsaro gabanin rantsar da shugaba Joe Biden mai jiran gado, yayin da birnin ke tunatar da wasu jami’ai irin kalubalen tsaron da aka gani a birane kamar Baghdad ko Kabul, ba mazaunin gwamnatin shugaban kasar daya daga cikin kasashen yammacin duniya ba.
Jami’an soja sun fada a jiya Juma’a cewa jimlar dakarun tsaron kasa na Amurka 18,000 ake sa ran zasu isa babban birnin na Amurka nan da kwanaki 4 masu zuwa, kari akan jami’an tsaro 7,000 da aka riga aka tura bayan tarzomar da aka yi ranar 6 ga wata Janairu lokacin da masu tsattsauran ra’ayi da ke goyon bayan shugaba Donald Trump mai barin gado suka mamaye ginin majalisar dokokin kasar.
Dakarun, tare da ‘yan sandan yankin, an basu sharuddan daukar mataki, wato lokacin da aka amince su yi amfani da karfi idan ta kama.