Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Jihar Pennsylvania A Zaben Shugaban Kasar Amurka


Jihar Penssylvania na da matukar muhinmanci a siyasar Amurka.

Jihar Pennsylvania na da matukar muhimanci a tarihin siyasar Amurka, don kuwa ita ce jihar da a cikin ta aka rubuta kundin tsarin mulkin kasar. Wanda haka yasa ake mata lakabi da “Constitutional State” a turance. Birnin Philadelphia na jihar, shine ya fara zama Fadar gwamnatin, kamun komawa Washington DC.

A bangaren siyasar Amurka ta yau, za a ga cewar kowace jiha tana da wakilai na Electoral College, wadanda suke wakiltar su a wajen zaben shugaban kasa. Yawan wakilan kowa ce jiha, na da muhinmaci a irin rawar da take takawa lokacin zabe.

Jihar California ce ke da wakilai 55, sai jihar Texas mai wakilai 38, haka jihar New York na da wakilai 29, daga nan kuma sai jihar Pennsylvania, wadda take da wakilai 20, hakan yasa duk wani dan takarar shugaban kasa ke burin lashe kuri’un jihar.

Don kuwa ko a bana jihar ta taka muhimmiyar rawa wajen bai wa Biden nasarar zama zababben shugaban kasar.

Don sanin irin muhimancin da jihar take da shi a siyasar kasar, ga abun da wani mazaunin jihar, Farfesa Gary Dean, ke cewa akan tasirin jihar a siyasar kasar.

"Sabo da yawan wakilai da ake da su a jihar, shi yasa a wannan zaben jihar ta zama tunga tsakanin Trump da Biden."

Ya kara da cewar "Saboda muhimancin jihar a zaben da ya gabata, Trump ya ce an yi magudi a jihar. Inda ya ke cewar, kuri’un da aka kada kamata yayi a ce shi ya lashe su."

Amma Gary Dean ya ce "tazarar da ke tsakanin su ta wuce a ce an yi magudi."

Na sake tambayar shi ko wai ana iya cewa gwamnatin Trump ta hada kan ‘yan kasar ko kuwa? Ya ce, "Ba shakka rarrabuwar kawuna ta kawo, yana yawo da abun da ya yadda da shi, don kuwa shi bukatar kansa ce kawai a gabansa."

Haka shima wani mai goyon bayan Trump cewa yayi "duk abun da ake fadi akansa ba gaskiya bane, ko cewar da ake yi ya tura magoya bayan shi su je majalisa, babu wani abu da yayi kama da hakan, kuma sai dai idan mutum baya son gaskiya, ya ce gwamnatin shi bata kawo cigaba a kasar ba.

Ba wai Amurkawa kadai ke tofa albarkacin bakunan suba, ga Dr. Nasiru Dan-Mowa wanda shi ma yake cewa. "Trump ya samu goyon bayan 'yan kauye, wadanda yayi musu alkawari, kuma ana iya cewa ya cika musu alkawuran da ya dauka. Ita kuwa gwamnati mai zuwa tana da banbancin ra'a yi da mai shudewa."

Idan Allah ya kai rai gobe ne da misalin karfe 12:00 na rana za a rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban kasa, da mataimakiyarsa mace ta farko kuma bakar fata a matsayin Mataimakiya, Kamala Harris. Saura da me kuma sai a sa ido don ganin kamun ludayinsu wajen shugabanci.

Ga cikakken rahoto a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG