Ayyukan farkon da zai fara suna cikin aikin kwanaki goma na sanya hannu a kan umarnin shugaban kasa da Biden zai yi na karkatar da akalar kasar daga alkibikar mulkin Trump ba tare da jiran amincewa daga majalisar dokoki ba.
A ranar Laraba, bayan an rantsar da shi, Biden zai soke haramcin shiga Amurka da Trump ya dora a kan baki daga kasashen da Musulmi suke da rinjayi, zai kuma mayar da Amurka a cikin yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris kana zai tilasta saka takunkumin rufe fuska a gine ginen gwamnatin tarayya da tafiye tafiye daga wata jiha zuwa wata jiha.
Wadannan na cikin akalla abubuwa da dama da Biden zai maida hankali a kai da zarar ya kama aiki a ranar farkonsa a fadar White House, a cewar shugaban ma’aikatansa mai jiran gado Ron Klain, a wata takarda da ya rubuta zuwa ga manyan ma’aikata.
Sauran matakan sun hada da fadada biyan rancen dalibai da aka dakatar da kuma daukar matakai na hana fitar da mutane daga gidajen su da kuma kawo karshen wahalhalu da mutane suka shiga a lokacin annoba.
“Wadannan dokokin umarnin shugaban kasa zasu kawo sauki ga miliyoyin Amurkawa da suka shiga halin kunci a lokacin annobar”, a cewar rubutacciyar takardar da Klain ya aike.
Idan gari ya waye ranar Alhamis, Klain ya ce Biden zai kuma sanya hannu a kan umarnin shugaban kasa a kan abubuwa masu alaka da barkewar COVID-19 da zummar sake bude makarantu da harkokin kasuwanci da kuma fadada gwajin cuta.
A ranar Juma’a, za a ga shugaban ya kuma sanya hannu a kan tallafi da zai kawo sauki ga matsalolin tattalin arziki sakamakon annobar coronavirus.