Hukumomin Mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun bayyana rashin jin dadi game da hukuncin kotun kasashen yammacin Afrika rainon Faransa UEMOA ta yanke dangane da bukatar janye takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar din da na ECOWAS a washe garin juyin Mulkin 26 ga watan Yuli.
Fannin noma ya samu koma-baya sakamakon sauyin yanayi a Nijar musamman idan aka yi la’akkari da cewa manoman sun fi dogara ne da noman damina. A kokarin samun wadata, kungiyar agaji ta kasa da kasa ta SWISSAID ta bullo da wani tsari na bunkasa noman rani.
Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne kwana guda bayan da wata tawagar manyan malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyarar shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce za su tuhumi hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum da laifin “cin amanar kasa” da kuma yi wa sha’anin tsaron kasa zagon kasa.
Da alamar wata kofa ta bude don tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da sojojin da su ka yi juyin mulki a janhuriyar Nijar da sauran masu ruwa da tsaki. Wannan ya biyo bayan ziyarar shiga tsakani da wasu manyan malaman Najeriya su ka kai.
Tawagar manyan malaman Islama na Najeriya da ta gana da shugaban gwamnatin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ta ayyana nasarar ziyarar.
Wata tawagar malaman addinin Islama ta ziyara a birnin Yamai a ranar Assabar inda suka gana da shugabannin mulkin sojin jamhuriyar Nijar da suka hada da Janar Abdourahamane Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.
Ganawar tasu na zuwa ne yayin da ECOWAS ke duba zabin daukan matakin soji a kan masu juyin mulki.
Wasu 'yan Nijar na ganin Faransa ba ta tabuka wani abin a-zo-a-gani a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci a kasar da ma yankin Sahel baki daya.
Domin Kari