NIAMEY, NIGER - Daruruwan mazauna birnin Yamai sun yi dandazo a yammacin Juma'a a kofar sansanin sojin Faransa da ke filin jirgin sama na Escadrille da nufin nuna bukatar Faransa ta kwashe dakarun da ta girke a Nijar da sunan yaki da ta'addanci.
Faransa na da sojojin sama da 1,000 jibge a kasar ta Nijar, wacce ke fama da rikicin shugabanci sanadiyyar juyin mulki da sojoji suka yi.
Wannan shi ne karon farko da 'yan Nijar ke samun damar yin dandazo a sansanin sojan na Faransa duk da ya ke an shafe shekaru suna nuna bukatar ficewar sojojin daga kasar.
Wasu 'yan kasar na ganin cewa Faransa ba ta tabuka wani abin a-zo-a-gani a yaki da ayyukan ta'addanci a Nijar da yankin Sahel baki daya.
A halin yanzu dai dangantaka na kara dagulewa ne a tsakanin Faransa da hukumomin Nijar tun bayan juyin mulkin da ya hambarar da zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.
Dandalin Mu Tattauna