Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Za Su Kai Bazoum Kotu


Hambararren Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum
Hambararren Shugaban Kasar Nijar Mohamed Bazoum

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce za su tuhumi hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum da laifin “cin amanar kasa” da kuma yi wa sha’anin tsaron kasa zagon kasa.

WASHINGTON, D.C. - Gwamnatin ta bayyana hakan ne cikin sanarwar da ta fitar sa’o’i bayan da ta ce a shirye take ta tattaunawa da kasashen yammacin Afirka ECOWAS, domin warware rikicin yankin da ke kara kamari.

Sojojin Juyin Mulkin Nijar
Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Idan har aka same shi da laifi, Bazoum na iya fuskantar hukuncin kisa, a cewar kundin tsarin hukunta laifuka na Nijar.

Kakakin sojojin Kanar Amadou Abdramane ya fada a gidan talabijin na kasar a daren Lahadin da ta gabata cewa, gwamnatin soja ta “tattara kwararan hujjoji don gurfanar da hambararren Shugaban kasar gaban kwararrun hukumomi na kasar da na kasashen waje, bisa laifin cin amanar kasa da kuma cin amanar kasa da hadin kan waje da gazawa wajen tsaron Nijar."

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Sanarwar ta ce manyan 'yan siyasar yammacin Afirka da "masu jagororinsu na kasa da kasa" sun yi zarge-zarge marasa tushe tare da yunkurin kawo cikas ga hobbasan da ake yi wajen warware rikicin cikin lumana domin su samu kofar aikewa da sojoji zuwa Nijar.

Ana tuhumar Bazoum ne biyo bayan da aka zarge shi da wata ganawa da ya yi da wadannan mutane.

Sanarwar ba ta bayyana takamaiman kasashen yammacin duniyan ba kuma ba ta ayyana ranar da za a yi shari'ar ba.

A ranar 26 ga watan Yuli ne wasu jami'an tsaron fadar Shugaban kasar suka hambarar da Bazoum, zababben Shugaban kasar ta Nijar, kuma tun a ranar watan ake tsare da shi tare da matarsa da ‘dansa a fadar Shugaban kasar da ke Yamai babban birnin kasar.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG