Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Musulunci Sun Tattauna Da Sojin Juyin Mulki A Nijar Domin Sulhu

Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar
Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar

Wata tawagar malaman addinin Islama ta ziyara a birnin Yamai a ranar Assabar inda suka gana da shugabannin mulkin sojin jamhuriyar Nijar da suka hada da Janar Abdourahamane Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.

NIAMEY, NIGER - Ganawar dai na da nufin share fage na shirye-shiryen zaman sulhu a tsakanin kungiyar kasashen Afrika ta yamma ECOWAS da sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum daga karagar mulki.

Saukar Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar
Saukar Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar

Malaman addinin kusan 20 daga dariku da akidu daban-daban ne suka ziyarci birnin na Yamai a da zummar neman hanyoyin kusanto banagrorin da ke takaddama sanadiyar juyin mulkin da soja suka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Tawagar a karkashin jagorancin shugaban kungiyar Izatul bidi’ah wa ikamatu sunnah, Sheik Abdullahi Bala Lau, haka ma ta nemi ganawa da Shugaba Mohamed Bazoum a inda ake tsare da shi sai dai haka ba ta ta cimma ruwa ba, kamar yadda Malan Aminu Sheik Dahiru Usman Bauchi ya shaidawa Muryar Amurka.

Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar
Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar

Firai Ministan rikon kwarya Ali Mahamane Lamine Zeine ya jaddada aniyar gwamnatinsa na zama akan teburin sulhu duk da yake ECOWAS ta kakaba wa Nijar takunkumi ba akan ka’ida ba inji shi.

A Lokacin Da Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar
A Lokacin Da Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar

Baya ga tankiyar siyasar da juyin mulkin ranar 26 ga watan yuli ya haifar a tsakanin Majalisar CNSP da kasashen duniya, a can cikin gida wasu ‘yan kasar na fakewa da zanga-zangar goyon bayan juyin mulkin don tafka ta’asa, lamarin da ya sa mai masaukin baki Sheik Abubakar Shehu Usman Sanam jan hankulan masu wannan danyen aiki.

Wasu Daga Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar
Wasu Daga Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar

Shugaba Mohamed Bazoum wanda a farkon mako bayanai suka yi nuni da cewa shi da iyalinsa na tsare cikin halin irin na muzantawa sakamakon rashin wutar lantarki da ruwa har ma da karincin abinci, ya samu ziyarar likitansa a cewar wasu rahotanni a ranar Assabar, wadanda suka kara da cewa likitan ya je masa da guzirin abinci, haka kuma ya ba da albishirin cewa babu wata alamar zullumi a tattare da Shugaban.

Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar
Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Da Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Tawagar Malaman Addinin Islama Daga Kasashen Yammacin Afirka Ta Kai Ziyarar Sulhu Nijar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:24 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG