A yau Talata ne shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar plato, ya tabbatar da cewa za'a gudunar da zaben 2019 a garin Quanpa, bayan offishin hukumar ya kama da wuta ya yin da wasu katunan mutane da kayan aiki suka kone.
‘Yan Najeriya sun fara jan hankalin ‘yan takara dake neman rike madafun iko da su maida hankali wajen fadin irin ayyukan da za su yi, in sun yi nasarar zabe maimakon yin yarfe wa junansu a lokacin yakin neman zabe.
Al'umomin jihar Nasarawa sun kira ga shugabannin da zasu zaba a zabe mai zuwa da su mayar da hankali kan ayyukan da za su inganta rayuwa.
‘Yan jarida a jahar pilato sun tunatar da kansu kan muhimmancin gabatar da rahotanni da zasu hana tada husuma a lokaci zabubbuka da za’a gudanar a Najeriya.
Uwargidan mataimakin shugaban Najeriya, Dolakpo Osinbajo ta gargadi al’ummar Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatansu don gudanar da zabe a zabubbukan da za’a gudanar a kasar.
Babbar kutun Jihar Pilato dake sauraron karar wadanda ake zargi da hannu kan kisan hafsan sojin nan, Manjo Janar Idris Alkali, ta bada belin mutane 21 daga cikin mutane 28 da aka gurfanar da su a gaban kotun.
Wasu matasa daga jihohin Pilato da Kogi sun bayyana kudirinsu na bijirewa shiga bangar siyasa da haddasa fitina a kasa.
Komitin da gwamnatin jahar Pilato ta kafa domin maida ‘yan gudun hijirar jihar zuwa garuruwansu na asali ya gano cewa fiye da mutane dubu hamsin da tara ne rikicin da ya auku a kananan hukumomi biyar na jihar ya shafa yayinda mutane dubu hamsin da dari biyu da goma sha biyu ke gudun hijira.
Hukumar ‘yan sandan jahar Filato ta sha alwashin gurfanar da mutane 19 da take zargi da kisan tsohon daraktan gudanarwa a helkwatar sojin Najeriya, janar Idris Alkali mai ritaya, a gaban kotu.
Rundunar sojin ta Najeriya ta yi kira ga sauran mutum biyun da ake nema, da su yi hanzarin mika kansu domin ana bibiyan duk inda suke.
Matan kungiyar zumuntar ECWA ta kasa da kasa sun kammala taronsu tare da gargadin junansu yadda zasu sarrafa iyalansu ta hanyar koyarwar Ubangiji don dakile matsalolin tsaro da ake fuskanta a sassa daban-daban na duniya.
Gwamnatin jahar Nasarawa tace kamfanin Siga da hamshakin dan kasuwannan Aliko Dangote ya kafa a yankin kudancin jahar zai ba mutane fiye da dubu talatin ayyukan yi.
A wani yunkuri na kwantar da hankalin jama'a da rundunar 'yan sandan jihar Filato ta sha alwashin yin aikinta babu sani ba sabo dangane da bacewar Janar Idris Alkali.
Masu ruwa da tsaki a jami’iyyar APC a jihar Nasarawa sunyi wani zama na musamman da ‘yan takarkaru da suka fafata a zaben fidda gwani don dinke duk wata baraka da ka iya kunno kai a jami’iyyar.
An gudanar da zaben shugabannai da kansiloli a kananan hukumomi goma sha uku na jahar Pilato, cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yawan makamai a hannun mutane ba bisa ka'ida ba da yayata labarun bogi na cikin abubuwan dake ruruta wutar rikici a jihar Filato kuma dole a yi maganinsu idan ana bukatar zaman lafiya
Hukumomin tsaro a jihar Filato sun bukaci al’umma dake ciki da wajen jihar da su gargadi matasa dake neman tayar da zaune tsaye a jihar su rungumi zaman lafiya.
Hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Pilato ta ayyana nanar goma ga watan gobe, wato Oktoba, don gudanar da zabe kananan hukumomi a jahar.
Rikicin da ake dangantawa da makiyaya da manoma a jihar Filato ya raba dubban mutane da muhallansu lamarin da ya jefa su cikin mummunan halin rayuwa.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta dukufa wajen wayar da kan al’umma matakan da zasu bi wajen kare kansu daga bala’in ambaliyar da ruwan sama ka iya haddasawa a jihohi.
Domin Kari