A Najeriya harkokin zabe na kara kankama, ‘yan takara kuma sai kara kaimi suke wajen janyo hankalin al’umma su zabe su saboda wasu ayyuka da suke niyyar yi musu na ci gaba.
A bangare guda kuma, al’ummar na bukatar shugabanni a matakin tarayya da jiha, su yi la’akari da ayyukan da zasu inganta rayuwarsu ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa, musamman a kasa irin Najeriya dake da dimbin albarkatun kasa.
Wakiliyar Muryar Amurka a jihar Nasarawa, Zainab Babaji, ta shiga garin Lafiya domin jin ra’yoyin mutane kan abin da suke so wadanda zasu zaba a zabe mai zuwa su yi musu.
A cewar mallam Dauda Alhaji Saleh, yana da kyau gwamnati ta samarwa da nakasassu wajen da za a ke horar da su sana’o’i domin dogaro da kai, da rage yawan barace-barace. Haka kuma zai yi matukar taimakawa idan gwamnati za ta ware wasu kudade tana baiwa nakasassu.
Inganta kiwon lafiya da samar da hanyoyin sufuri na daga cikin bukatun Usman Abdullahi, wanda kuma ya yabawa gwamna mai ci a yanzu kan kokarin da ya yi ga batun tsaro a jihar Nasarawa.
Baya ga sauraron ra’ayoyin jama’a, Zainab ta tambayi gwamna Umaru Tanko Almakura, ko wacce wasiya zai barwa al’ummar jiharsa ganin cewa wa’adinsa na biyu ya kusa karewa.
Da yake amsa tambayar Almakura, ya ce karfafa zuciya bisa kyawawan halaye da ayyuka da kuma tsaida gaskiya da rikon amana, wanda su ne zasu tabbatar da zaman lafiya a jihar Nasarawa.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Facebook Forum