A watan Yulin wannan shekara ne dai gwamnatin jahar Pilato ta kafa kwamitin don gano wuraren da rikicin ya shafa da zummar maida wadanda ke gudun hijira zuwa mahallansu na asali.
Kananan hukumomin da kwamitin yayi nazari a kansu sun hada da Jos ta Arewa, Bassa, Riyom, Barkin Ladi da Bokkos.
Shugaban kwamitin Air Vice Marshal, Bala Danbaba mai ritaya yace sun gana da masu ruwa da tsaki, sun zaga wuraren da rikicin ya auku, sun karbi bayanai daga al’ummomin da rikicin ya shafa.
Gwamnan jahar Pilato, Simon Lalong yace gwamnatinsa zata yi nazarin rahoton ta kuma fidda wani tsari da zata aiwatar nan bada jimawa ba da zai yi adalci wa kowa.
Ga rahoton da wakiliyar mu Zainab Babaji ta aiko mana daga Jos:
Facebook Forum