Rahotanni daga Najeriya na cewa dakarun kasar sun gano inda aka jefar da gawar Gen. Idris Alkali mai ritaya, wanda aka kashe a yankin Jos ta Kudu a jihar Pilato a farkon watan nan.
An gano gawar ce a cikin wata tsohuwar rijiya a kauyen da ake kira Guchwet da ke Gundumar Shen a cewar kafafen yada labaran Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da safiyar yau Laraba aka kwashe ruwan rijiyar inda aka gano gawar.
Kwamandan runduna ta 3 ta Maxwell Kobe Cantonment da ke rukuba a Jos, Brigadier Gen. Umar Muhammad, wanda yana daya daga cikin masu binciken, ya ce, daya daga cikin mutane takwas da ake nema ruwa a jallo ne wanda ya mika kansa, ya bayar da bayanan inda aka yar da gawar.
Yanzu haka ana rike da mutane shida daga cikin takwas da ake nemansu ido rufe.
Rundunar sojin ta Najeriya ta yi kira ga sauran mutum biyun, da su yi hanzarin mika kansu domin ana bibiyan duk inda suke.
A ranar 3 ga watan Satumba aka nemi Gen. Alkali aka rasa a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja.
An yi amfani da wayarsa wajen bin diddigin inda ya tsaya a karshe.
Daga baya aka gano motarsa a cikin wani kududdufi da wasu kayayyakinsa, lamarin da ya sa aka shiga aikin yashe ruwan wanda ke Dura Du.
A makon da ya gabata, rundunar sojin ta Najeriya ta gano wani kabari mara zurfi da aka fara binne shi amma kuma wadanda suka kashe suka sauya mai wuri, bayan da suka ga an tsananta bincike.
A gefe guda kuwa lauyan dake kare al’ummar da ake zaton lamarin ya auku a yankinsu ne, Barista Godfree Mathew yace suna bukata ‘yan sanda ne su gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda dokar kasa ta ayyana.
A cikin hirarsu da wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji, lauyan yace, al'ummar kauyen da aka sami gawarsa sun kauracewa garin sakamakon hare haren da ake kai masu sabili da haka za a yi riga mallam masallaci idan aka dora masu alhaki ba tare da gudanar da cikakken bincike ba .
Saurari cikakken rahoton Zainab.
Facebook Forum