An kai wani mummunan hari a wani dadadden masallacin Sufaye mai suna Data Darbar da ke birnin Lahore na kasar Pakistan a yau dinnan Laraba.
Rundunar sojojin saman Najeriya ta kaddamar da wani Sabon sansani a Birnin Gwari, tare da tura jiragen yaki a yankin don sake sabon damarar ci gaba da tunkarar ta'addancin 'yan bindiga dadi.
Firayim Ministar kasar New Zealand na dab da zama amarya bayan da saurayin da ya dade yana nemanta yayi mata tayin aure.
Fadar shugaban Amurka ta White House ta ce a mako mai zuwa wasu manyan jami’an Amurka za su je kasar China, domin ci gaba da tattaunawa don samar da masalaha tsakanin kasashen biyu a fannin cinikayya.
Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong-un, ya isa yankin gabashin Rasha don ganawar sa ta farko da Vladimir Putin, wanda Kim ya ce shine mataki na farko don kusantar dangantaka da Moscow.
Mai bincike na musamman Robert Mueller ya yi bincike game da lokuta 11 wanda ya ke kyautata zato cewa Shugaba Donald Trump ya karya doka a kokarin dakatar da bincikensa.
Firayim Ministan kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga da dukan mambobin gwamnatinsa sun yi murabus a jiya Alhamis.
A yau Laraba ne ‘yan kasar Indonesia suka fara kada kuri’a wanda ya zama zabe mafi girma da za’a gudanar a cikin rana guda.
‘Yar Shugaban kasar Amurka Donald Trump kuma mai ba da shawarwari a fadar White House, Ivanka, ta ziyarci kasar Ivory Coast a ziyarar aiki ta kwanaki hudu da take yi domin inganta tattalin arzikin mata a yankin yammacin Afrika.
Rahotanni a baya-bayan nan na cewa, kudin dake asusun ajiya na kasar China zai kare a shekara ta 2035, wannan ya janyo cece kuce a hanyar sadarwa ta Internet.
Masu zanga-zanga a Khartoum suna ci gaba da neman shugaban kasar Omar al-Bashir da yayi murabus, a cigaba da zaman da suke yi a hedkwatar sojan kasar, inda aka ji karar harbin bindiga.
Akwai alamun dake nuna cewa mai yiyuwa ne Firma Ministan Israili Benjamin Netanyahu zai yi nasarar samun wa’adi na 5 na mulki bayan da sakamakon zabe ya nuna cewa jami’yyar sa ta Likud ne zata iya lashe zaben.
Domin Kari