Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya gayawa shugabannin kungiyar tsaron Turai ta NATO cewa dole ne kungiyar, mai kasashe 29 a cikinta, ta fito da wani sabon salo na yadda zata tunkari sabbabin abubuwa masu barazana ga zaman lafiya a duniya.
Lokacin da yake jawabin bude babban taron da ministocin harakokin wajen Turai suka fara tun jiya a Washington don bikin cikar shekaru 70 da kafa kungiyar ta NATO, Pompeo ya gaya musu cewa wajibi ne a san yadda kasashen nasu zasu fuskanci duk wata barazana da zata iya fitowa daga kasashe irinsu Rasha da China, musamman barazanar da za’a yi ta kai hare-hare ta cikin duniyar gizo, ko ga ma’aikatun makamashi, ko kuma ta fuskar soja.
Shima, da yake jawabi jiya ga taron hadin gwiwa na Majalisun Dokoki biyu na Amurka, babban sakataren NATO, Jen Stoltenberg, ya ja kunnen Amurka da ta kwana cikin shirin fuskantar karin tsokana daga Rasha.
Facebook Forum