Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ta ce: "Shugaban kasa ya amince da murabus din na firaministan kasar da na mambobin gwamnatin sa."
Wannan mataki ya zo ne bayan tashe tashen hankula a yankin tsakiyar kasar, ciki har da kisan gilla a watan jiya na Fulani 160, wanda ake zargin mafarauta na Dogon ne suka aikata.
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar rahoton cewa, a cikin shekarar da ta wuce, fada tsakanin Fulani da al’umar Dogon ya janyo mutuwar mata da yara da maza har guda 600.
Makonni biyu da suka wuce an yi zanga-zanga a garin Bamako, babban birnin kasar, don nuna rashin amincewa da rashin ikon gwamnati na hana aukuwar tashe tashen hankula.
Facebook Forum