Wani sabon rahoto na Majalisar Dinkin Duniya ya ce watanni shida bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 12 ga Satumba, shekarar 2018, har yanzu babu wanda aka sake daga cikin fursunonin siyasa wadanda suke tsare a Sudan ta kudu.
Biyu daga cikin manyan masu sukar gwamnati, Aggrey Idri, mamban kungiyar SPLM-IO, da Dong Samuel Luak, lauya mai kare hakkin bil adama sun bace a ranar 23 zuwa 24 ga watan Janairu, shekarar 2017, daga Nairobi.
Masana a Majalisar dinkin duniya kan harkokin kasar Sudan ta Kudu sun bayyana cewa, gwamnatin Sudan ta Kudu ta karyata cewa ta san inda Idri da Luak suke.
Facebook Forum