Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Benjamin Netanyahu Ya Yi Nasarar Samun Wa’adi Na Biyar


Israel Election
Israel Election

Akwai alamun dake nuna cewa mai yiyuwa ne Firma Ministan Israili Benjamin Netanyahu zai yi nasarar samun wa’adi na 5 na mulki bayan da sakamakon zabe ya nuna cewa jami’yyar sa ta Likud ne zata iya lashe zaben.

Bayan an kidaya kashi 97 cikin 100 na kuri’in da aka jefa a zaben, Jam’iyyar Likud ta cimma jam’iyyar Blue and White ta tsohon kwamandan sojan Isra’ila, Benny Gantz.

Ya zama dole a kafa gwamnatin hadin gwiwa sabo da babu jam’iyyan da zata iya samun rinjaye a Majalisar Dokokin Isra’ila da ake kira Knesset. Likud da kawayen ta za su iya samun kujeru 65 daga cikin kujerun majalisar guda 120.

Kowacce daga cikin jam’iyyun biyu tayi ikrarin cewa itace ta lashe zaben.


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG