Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Turai Sun Kai Ziyara Wasu Kasashen Afrika


Shugabar kasar Jamus Angela Merkel da sakataren harakokin wajen Biritaniya Jeremy Hunt na ziyarar kasashe daban-daban na Afrika a cikin wannan makon.

Alamar dake nuna cewa kasashen Yammacin Turai sun fara neman wasu hanyoyin fadada harkokinsu na tattalin arziki da kasuwanci, da batun shige da ficcen bakin haure da kuma harkokin tsaro.

Ita dai shugabar Jamus, Merkel, yanzu haka tana ziyartar kasashen Burkina Faso, Nijer da Mali, inda take bayyana shirin Jamus na zuba jarin dala miliyan 68 don bunkasa ayyukan ‘yan sanda da sauran ma’aikatan tsaro.

Yanzu haka akwai sojojin Jamus fiye da dubu daya dake kasashen Afrika suna aikin kiyaye zaman lafiya da kuma yaki da kungiyoyin fafutikar Islama dake kasashen.

Yayinda hakan ke faruwa, shima Sakataren harakokin Wajen Birtaniya Jeremy Hunt yana Afrika don kaddamar da wani yunkuri na inganta dangatakar diflomasiya tsakanin Birtaniya da kasashen, inda har zai bude sababbin ma’aikatun jakadancin Ingila a kasashen Nijar da Chadi ya kuma bayyana shirin kashe fiye da dala miliyan 5 wajen koyar da harshen turancin Ingilishi.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG