Mu’amula tsakanin tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da shugaba Muhammadu Buhari ta shiga wani hali.
Majalisar tattalin arziki karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ta yi wani babban taronta a Abuja inda ta bankado wata badakala da ta shafi wasu kamfanonin gwamnatin tarayya.
Majalisar dake kula da tattalin arziki ta Najeriya ta bayar da umarnin cewa a dakatar da kiwo tsakanin kasa da kasa, domin kawar da tashe-tashen hankulan da ake fuskanta a Najeriya.
Najeriya na da shirin yin sulhu da mabiya shi'a bayan arrangamar da ya auku tsakanin 'yan sanda da 'yan shi'an a ranar Talata, inda aka raunata wasu tare da kama mabiya addinin da dama.
Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan lambar yabo ta bogi da ake cewa an baiwa shugaba Mohammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Mohmmadu Buhari yayi ganawa ta musamman a fadar gwamnati da ‘yan matan Dapchi da iyayensu, inda ya bada tabbatacin cewa gwamnati zata kare sauran makarantu da kuma tabbatar da an inganta sha’anin ilimi a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Kama daga majalisar wakilan Najeriya da masu fafutikar kare hakkin dan Adam a Najeriya tamkar kowa na cikin rudani a kan badakalar dake faruwa a hukumar leken asirin kasashen waje, NIA inda yanzu gwamnatin Buhari ta sallami tsohon mukaddashin shugsbsn hukumsr daga aiki
Halayen Shugaban Amurka Donald Trump sun sa 'yan Najeriya na ganin ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka zuwa nahiyar Afirka musamman Najeriya ba zata yi wani tasiri ba domin shugaban na iya birkitar da duk wani shiri aka yi da kasarsa.
Jami'an tsaro na farin kaya DSS da NIA sun yi wa gidan mukaddashin shugaban NIA kawanya lamarin da ya sa kungiyoyin da ke tabbatar anyi adalci da yaki da cin hanci da rashawa ke ganin gwamnatin Najeriya ba da gaske ta ke yi ba akan yaki da cin hanci da rashawa ba.
A wani kokari na farfado da kamfanin sufurin jiragen saman Najeriya da kuma kafa wani kawance da zai samar da kamfani na bai-daya a tsakanin kasashen Afirka, Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai tsara aitawar da wannan buri.
Femi Adesina, kakakin shugaba Muhammadu Buhari, yace sabon atusayen mai suna Operation Cat Race" za a kaddamar da shi cikin wannan makon a jihohin dake fama da fitina a yankin arewa ta tsakiya.