Da yake mayar da martani kan wannan jita-jita da ta mamaye Najeriya, kakaki a fadar gwamnatin tarayya mallam Garba Shehu, ya ce ba dai dai bane a dinga soki buruzu akan maganar da bata da kanshin gaskiya a ciki.
A cewar mallam Garba Shehu kungiyar da ta baiwa shugaba Buhari lambar yabo, kungiyar ce ta ‘yan asalin Afirka masu zama a Amurka, ba wai cibiyar nan bace ta The King Center ta shahararren bakar fatar Amurka wanda yayi gagwarmayar yaki da wariya da ake yiwa bakaken fata.
Kamar yadda kakakin gwamnatin ya bayyana, akwai rashin fahimta kan abin da ya faru, “kamar mutum ne ace jami’ar Maiduguri ta bashi digiri, sai kuma wani ya baza karya yace jam’ar Sokoto ta bashi digiri, kaga idan jami’ar Sokoto bata bashi digiri ba ai dole ta fito ta nisanta kanta daga maganar.” A cewar mallam Garba Shehu.
Ya ci gaba da cewa matar da ta jagoranci mika lambar yabo ga shugaba Buhari, sirika ce ga Martin Luther King kuma batace cibiyar The King Center ce ta turo ta ba, kungiyar ‘yan asalin Afirka mazauna Amurka ne suka baiwa baiwa shugaban lambar yabo akan yaki da rashawa da cin hanci.
Wasu bayanai da ke fitowa a kafafen sada zumunta na nuni da cewa cibiyar The King Center ta fito fili ta nisanta kanta da wannan lambar yabo da aka baiwa shugaba Buhari.
Facebook Forum