Wannan umarni na daya daga cikin muhimman batutuwan da ita Majalisar ta amince akai, bayan da ministan Noma ya gabatar da wani rahotan kwamitin bincike da aka kafa domin duba hanyoyin da za a kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.
Majalisar ta sake duba tsarin shige da fice na ECOWAS wanda bakin makiyaya ke shiga Najeriya da shanu masu yawa, kuma suna janyo matsala. An dai yanke hukuncin dakatar da wannan tsari yanzu haka.
Dangane da wannan shawarar da aka yanke gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru, ya ce matsayin da aka dauka a taron shine a baiwa gwamnonin dake jihohin dake fama da rikice-rikicen shawarar kebe guraren kiwo.
Za a fara yin hakan ne a jihar Kaduna, kafin akai ga sauran jihohin dake fama da matsalar domin a zaunar da makiyaya guri guda.
Domin karin bayani saurari rahotan Umar Faruk Musa.
Facebook Forum