Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Fara Shirin Kafa Kamfanin Jirgin Sama Na Fasinja A Afirka


A wani kokari na farfado da kamfanin sufurin jiragen saman Najeriya da kuma kafa wani kawance da zai samar da kamfani na bai-daya a tsakanin kasashen Afirka, Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai tsara aitawar da wannan buri.

Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai tsara yadda Najeriya za ta kafa kamfanin sufuri na jirgen sama.

Wannan wani mataki ne a bangaren Najeriya, na cimma wata yarjejeniya da kasashen kungiyar Afirka ta AU ta kulla na samar da kamfanin sufurin jiragen sama na bai-daya ko kuma wadanda za su rika kawance da juna

Minista mai kula da sha’anin sufurin sama na Najeriya, Hadi Sirika ne ya bayyana hakan yayin wata hira da Muryar Amurka.

“Wannan alfanun da zai kawo wa Najeriya yana da yawa saboda dumbin al’uma da muke da ita mai yawan miliyan 180.” Inji Sirika.

Ministan ya kara da cewa, idan Najeriya ta kafa kamfanin jiragen sama masu kwari “sune za su rika tafiya kasashen nan na Masar, su tafi Morocco da Algeria da Afirka ta Kudu.”

A cewar ministan, tun a 1999 aka rattaba hanu akan wannan shiri na kafa kamfanin jiragen sama a Afirka da za su rika kwance da juna, amma Allah bai yi ba sai a wannan karon.

Sai dai wani batu da ka iya zama barazana ga wannan buri shi ne, ta yadda kamfanonin za su iya gogayya da takwarorinsu na kasashen da ke wajen nahiyar, kamar na turai.

Amma, ministan ya ce, wannan ba kalubale ba ne domin a cewarsa, “misali, tikitinka na Ethiopia Airline, za ka iya amfani da shi a Nigerian Airline, wannan zai ba mu dama mu yi gogayya da su.”

Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG