Jami'an hukumar NIA da na DSS sun yi wa gidan mukaddashin shugaban hukumar leken asirin kasashen waje, NIA Muhammad Dauda, kawanya a Abuja.
Kwanaki biyu ke nan a jere da gidan yake cikin wannan hali.
Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar wakilai tarayya da hukumar EFCC ke biciken badakalar nan inda aka gano miliyoyin dalar Amurka a gidan tsohon shugaban hukumar Oke lamarin da ya yi sanadiyar tsigeshi daga mukaminsa.
Amma shugaban kungiyar Patriotic Front ta Najeriya, kungiyar dake yaki da rashin adalci a Najeriya, Malam Tijjani Isa ya ce lamarin na da ban tsoro. Ya na ganin an yi hakan ne a tsorata shi Muhammad Dauda kada ya ci gaba da tona asirin badakalar da ta faru a hukumar. Ya ce abun mamaki shi ne Ambassador Oke da aka sameshi da hannu dumu-dumu a badakalar yana zaune gidan gwamnati tare da masu kare lafiyarsa.
Kungiyarsu zata yi taro a Abuja ta tabbatar cewa ba'a raunata binciken ba ba'a kuma hana shi Muhammad Dauda ci gaba da fallasa abun da ya sani.
Shi ma Malam Awal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar Transparency International reshen Najeriya ya ce lamarin ya sake tabbatar masu cin hanci da rashawa na nan da rai a kasar. Hukumomi sun daurewa cin hanci da rashawa gindi.
A saurari karin bayani a rahoton Umar Faruk Musa
Facebook Forum