Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa sulhu da ake yi da ‘yan kungiyar Boko Haram zai ci gaba da gudana har sai lokacin da aka kawo karshen tashin hankali a kasar.
Da yake karin haske dangane da jawabin da shugaba Mohammadu Buhari yayi, Mallam Lawal Daura, babban daraktan hukumar tsaro ta cikin gida DSS, ya nuna cewa mu’amular da yanzu haka aka kulla da Boko Haram za ta sa a sake samun faruwar irin wannan lamari ba.
Lawan Daura ya kara jaddada cewa gwamnati bata baiwa kungiyar Boko Haram ko sisin kwabo, kamar yadda wasu ‘yan kasar ke zargin hakan ya faru.
Shi kuma ‘dan Majalisar Dattawa daga jihar Yobe Bukar Abba, wanda ya halarci ganawar da Buhari ya yi da ‘yan matan Dapchi da iyayensu, ya amince da matakin da gwamnatin Borno ta ‘dauka na rufe makarantun kwana a jihar.
Yanzu haka dai ‘yan matan da iyayensu sun saka ido domin ganin irin tanadin da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin Yobe za suyi wajen inganta iliminsu da kuma samar da tsaro kamar yadda shugaba Buhari ya yi alkawarin yi a jawabinsa.
Domin karin bayani ga rahotan Umar Faruk Musa.
Facebook Forum