A jamhuriyar Nijer an cimma yarjejeniya a tsakanin hukumar zaben kasar da kamfanin Gemalto na kasar Faransa wace a karkashinta kamfanin zai hada kundin rajistar zabe irin na zamani akan biliyon 19.6 na cfa. aikin da ake saran kammalawa nan da watanni 16 masu zuwa.
yanzu haka ofishin ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar ya bukaci gwamnan jihar Tilabery da ya janye dokar ta-baci da ya kafa a jihar.
Bayanai sun yi nuni da cewa amfani da wayar salula akan aiki na daga cikin dalilan dake haifar da rashin samun cikakiyar nutsuwa a wajen jami’an tsaro.
'Yan kasar Nijar sun yi kira ga al'umomin Najeriya da 'yan siyasa su kaucewa duk wasu hanyoyi da zasu haddasa tashin hankali a kasar lokacin zabe.
Ya yin da shirye-shiryen zabe ya kankama a Najeriya, masu sharshi a jamhuriyar Nijar sun fara bayyana matsayinsu a game faruwar wasu abubuwan da ke nuna alamun Nijar na goyon bayan daya daga cikin ‘yan takarar zaben shugaban kasa mai zuwa.
Hukumar yaki da cin hanci ta jamhuriyar Nijer wato HALCIA da takwararta ta Najeriya wato EFCC sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya a yau a birnin yamai da nufin farautar mahandama a kasashen biyu makwaftan juna.
Amurka na kan gaba wajan taimakawa sojojin jamhuriyar Nijar, inda ko a shekarar 2016 ta tallafa mu su da jiragen yaki guda biyu tare da horar da su, yanzu haka ta gina mu su wata cibiyar samar da bayanai domin ci gaba da yaki da ta'addanci.
A Jamhuriyar Nijar yau akawunan kotu sun fara yajin aikin kwanaki biyu na gargadi da gwamanati, akan wasu tarin matsaloli da suka yi alkawarin magance musu a yayin zaman sulhu da su ka yi da gwamnati a shekara 2014.
Yan sandan Janhuriyar Nijar sun dakile wani hari da yan bindiga su ka kai a yankin Tilaberi, inda suka kashe dan bindiga daya.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana komawar kasar cikin kungiyar kasashe masu arzikin ma'adanai ta duniya wato ITIE. Hukumonin kasar sun jaddada cewa kasar za ta yi matukar amfana da komawa kungiyar.
Tun bayan da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bada dama masu saka jari daga kasashen waje su zo su saka jari a kamfanin SONITEXTILE, wanda daga baya ya koma SOTEX, yanzu haka "yan kasar China sun janye kudadensu, lamarin da ya sa ma'aikatan kamfanin ba su samun albashi.
Yanzu haka bankin Musulunci na IDP ya dauki nauyin wasu muhimman ayyukan raya kasa a Jamhuriyar Nijar.
Shugaban majalisar ministocin Italiya ya gudanar da ziyarar aiki ta wuni guda a jiya talata a jamhuriyar Nijer inda suka tantauna akan wadansu mahiman batutuwa
Kwararrun likitoci a Jamhuriyar Nijar sun yi kira da Gwamnati da ta tashi tsaye domin magance irin matsalolin da su ke addabar su.
Ana kara samun cigaba da zaman lafiya a wasu kauyukan birnin Tilaberi a Jamhuriyar Nijar.
Wani Rahoto ya jaddada cewar ana samun karuwar ayyukan cin hanci da rashawa a kasar Nijar.
Yayin da Jam’iyyar adawa ta CDS RAHAMA ke shagulugulan cika shekaru 27 da kafuwarta shuwagabanin jam’iyar sun kudiri aniyar mayar da ita a matsayinta na fil azal.
Hukumar ‘yan sandan da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta cafke wasu mutane lokacin da suke kokarin shiga kasar jamhuriyyar Niger da wasu dinbin kwayoyi.
Domin Kari