Lura da yadda mahandama dukiyar jama’a ke amfani da hanyoyin kasa don boye abubuwan da suka wawure a kasashensu na asali ya sa hukumar HALCIA da takwarar ta Najeriya EFCC kulla yarjejeniya wace a karkashinta Najeriya da Nijer zasu yi aikin hadin guiwa da zummar tunkarar wannan kalubale inji shugaban hukumar EFFCC Ibrahim Magu.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA mai shara’a ABDOURAHMAN GHOUSMAN ya bayyana cewa yarjejeniyar hukumomin biyu za ta yi tasiri sosai a yakin da suka kaddamar da barayin dukiyar jama’a…
Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA mai shari’a Abdourahaman Ghousman ya bayyana cewa yarjejeniyar hukumomin biyu za ta yi tasiri sosai a yakin da suka kaddamar akan barayin dukiyar jama’a.
Kamar yadda gwamnatoci ke kara tsaurara matakan dakile hanyoyin cin hanci haka su ma mahandama dukiyar jama’a ke kokarin bullo da dabarun kaucewa dukkan wani tarkon da aka dana, sabili kenan da shugaban reshen transparency international a Nijer Mamman Wada ke gargadin mahukunta.
Rahoton Transparency International na shekarar da ta gabata ya saka Nijer da Najeriya a sahun kasashen da suka yi wani dan karamin hobbasa akan maganar yaki da cin hanci yayinda kungiyoyin cikin gida ke kallon dalilan siyasa a matsayin wani tarnakin da ke hanawa jami’an yaki da cin hanci motsawa.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum