A jamhuriyar Nijar dakarun tsaron kasar sun yi nasarar hallaka daruruwan mayakan Boko Haram, a yayin wani farmakin sama da na kasa da suka kai daga ranar 28 ga watan Disambar da ta gabata, kawo zuwa jiya 2 ga watan Janairu a tsibirin tafkin Chadi da gabar Kogin Komadugu. Yayin da sanarwar tace ba wani sojan kasar da ya samu ko da rauni abinda ya matukar faranta ran ‘yan kasar.
Sanarwar wace aka bayar a daren jiya a kafar Talabijin mallakar Gwamnatin Nijar na cewa dakarun tsaron kasar sun fatattaki ‘yan kungiyar Boko Haram a tsibiran tafkin Chadi da gabar kogin Komadougou, a yayin wani gagagrumin farmakin da suka kaddamar a ranar 28 ga watan Disamba.
Dakarun sojin Nijar, sun sama damar hallaka 'yan kungiyar ta Boko Haram sama da 200, sai sojin kasa suka samu damar hallaka karin 'yan ta'addan 87, a cewar sanarwa wace ta kara da cewa askarawan na Nijar sun lalata kwale- kwale 9, sannan sun karbe motoci 3 da wasu tarin rokoki da bindigogi, hade da dubban harsasai da wasu magungunan da ake jerawa a sahun miyagun kwayoyi.
Hada gwiwa tsakanin Najeriya da makwaftanta a wannan yaki dake kokarin gagarar kundila, wani abu ne da ya zama dole ga gwamnatocin kasashen yankin tafkin Chadi su dauki kwararan matakai, muddin ana son murkushe Boko Haram a dan takadirin lokaci inji masana.
Ga rahoton Sule Mumuni Barma daga jamhuriyyar Nijar.
Facebook Forum