Wata cibiyar nazari da bincike a kasashen Afrika da ake kira Afro Barometre, ta fitar da wani rahoton binciken da ta gudanar a jamhuriyar Nijar, bayan wani zagayen yankunan kasar da yaba jami’an cibiyar damar hada ra’ayoyin jama’a akan batun cin hanci da rashawa.
Kimanin mutane 1,200 da suka hada da mata 600 maza 600 ne cibiyar nazari da bincike ta Afro ta tuntuba, a yayin binciken da ta gudanar a yankuna 8 na jamhuriyar Nijar, a matsayin wani ma’aunin tantance mizanin cin hanci a wannan kasar.
Kashi 60 daga cikin 100 na ‘yan Nijar na ganin cin hanci yayi katutu a galibin fannoni na ofisoshin hukumomi, sai dai jami’an jandarma da ‘yan sanda ne ke kan gaba wajen aikata wata haramtaciyar dabi’ar a cewar wannan rahoto.
Sai dai ra’yoyin jama’a sun ban-banta akan wannan al’amarin, a cewar Malan Soumaila, akwai kamshin gaskiya a tare da wannan rahoto na Afro.
Kawo yanzu ba wani martani daga wajen hukumomi akan wannan rahoton, amma a watannin baya ofisoshin ministan cikin gida da na shari’a, sun shirya wani taro wanda ya hada jami’an tsaro da masu kare hakkin jama’a, don nazarin hanyoyin magance matsalar cin hanci akan hanyoyin zirga zirga.
Da zummar samo hanyoyin ci gaba da daukan matakan kawo karshen karbar na goro daga hannun talakawa, dabi’ar da ake ganin a halin yanzu ta shafi kowane fanni na harakokin yau da kullun a kasar ta Nijar.
Ga rahoton wakilin Muryar Amurka daga birnin Yamai Sile Mumumi Barma.
Facebook Forum