A janhuriyar Nijar, yayin da a jiya Asabar jam’iyar CDS RAHAMA ke shagulugulan cika shekaru 27 da kafuwarta, shuwagabaninta sun kudiri aniyar mayar da ita a matsayinta na fil azal don ganin ta yi gogayyar neman mulkin kasa da manyan jam’iyyun kasar a zabukan 2021.
Cikin yanayin rarabuwar kawuna magoya bayan CDS RAHAMA suka gudanar da shagulgulan cikar wannan jam’iya shekaru 27 da kafuwa, sakamakon rikicin dake ci gaba da kara ta’azzara tsakanin wasu shuwagabaninta akan maganar cancantar shugabanci.
Bangaren Me Madouguo Boubacar, a wata sanarwar da ya fitar, ya nuna damuwa a game da halin tagayyar da wannan jam’iya ta tsinci kanta, ciki kamar yadda mataimakin shugaban jam’iyyar, Dr. Seidou Oumarou ya bayyana.
Bangaren Abdou Labo, wanda ya shirya nasa bukin na daban, ya alakanta koma bayan jam’iyar ta CDS RAHAMA, da abinda ya kira rashin hakurin wasu abokan tafiya.
kusoshin CDS na sassan kasa sun sha alwashin samarda hanyoyin warware rigingimun dake dabaibaye wannan jam’iya.
To amma a nasu bangaren matan RAHAMA irinsu MME Warkou Rakia Maidaji na ganin dole ne magabatan jam’iya su canza hali.
Tuni matasa suka bullo da wata dabarar tayar da takwarorinsu daga barci inji Ila Moussa shugaban matasan CDS RAHAMA yankin Dosso.
Ga wakilin Muryar Amurka a Yamai, Sule Barma, da cikakken rahoton:
Facebook Forum