Hukumomin tsaro a jamhuriyar Nijer sun umurci jami’an tsaro su dakatar da amfani da wayoyin hannu da dukkan wata na’urar nadar hoto a fagen fama da nufin kawo karshen dabi’ar fallasa hotuna da bayanan sirrin tsaro a shafikan sada zumunta.
A takardar da ya aikewa kwamnadojin kula da sha’anin tsaro babban komandan rundunar mayakan Nijer Ahmed Mohammad, ya sanarda su cewa daga yanzu haramun ne jami’an tsaro su yi amfani da wayar cellula ko na’urar daukan hoto ko ta nadar bidiyo a yayin da suke fagen daga bayan lura da yadda wasu jami’an tsaro ke fallasa abubuwan da ba su dace ba a shafikan sada zumunta a wannan lokacin da kasar Nijer ke neman bakin zaren matsalar ta’addanci.
Daukan matakan yiwa umurin na hafsan hafsoshin kasa biyayya da ma maganar dorewar wannan tsari ya zama wajibi ga mahukuntan Nijer don ganin an yi nasara a yakin da kasar ta kaddamar da kungiyoyin ta’addancin da suka addabi yankin sahel.
Wallafa hotunan dake da nasaba da aiyukan tsaro a kafar facebook ko rarraba wasu bayanan sirrin soja ta hanyar whatsapp wani abu ne da ke kokarin samun gindin zama a nan Nijer kamar yadda a makon jiya aka yi ta yada abubuwan da suka shafi fadan da aka kafsa a tsakanin sojan wannan kasa da ‘yan ta’addan Boko Haram a garin Chetimarin yankin Diffa.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum