Rahotanni na bayyana cewa ‘yan bindiga na gallazawa bakaken fatar da suka yi garkuwa da su a kasar Libya, inda sukan nemi a biya kudin fansa.
A 'yan kwanakin, wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, ya nuna wasu larabawa dauke da bindigogi sun saka wasu bakaken fata a gaba a dokar daji sun tisa keyarsu a wani yanayi mai kama da na wulakanci.
Tuni masu mahawara a shafukan sada zumunta ke alakanta wannan lamari da cin zarafin da ake zargin ‘yan bindigar Libya na yi wa bakaken fata.
Wani da bai so a ambaci sunansa ba da ke yi wa Muryar Amurka bayani ta hanyar sadarwar Whatsapp, ya tabbatar da faruwar wasu abubuwa makamantan hakan.
Kungiyar kare hakkin bakin haure ONG Jimed wacce ta yi Allah wadai da wannan al’amari a wata sanarwar da ta fitar, ta bukaci gwamnatocin Afirka musamman hukumomin Nijar da su gaggauta daukan matakan kariya ga ‘yan ciranin kasar a Libya.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta nuna rashin ji dadin a game da abubuwan dake wakana, ta alakanta wannan al’amari da aika aikar ‘yan damfarar dake safarar bakin haure, kamar yadda ministan harakokin wajen kasa Kalla Hankourao ya bayyanama muryar Amurka.
A cewar minista Kalla Hankourao, yanzu haka hukumomin na Nijar na shirye- shiryen wani taron gaggawa da takwarorinsu na Libya da nufin daukan matakan murkushe wannan matsala.
Domin jin karin bayani, saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai.
Facebook Forum