Yayin da al’ummar Ghana ke shirin halartar rumfunan zabe a ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024, ‘yan kasar mazauna Jamhuriyar Nijar sun bayyana manyan matsalolin da suke fatan sabuwar gwamnatin da za ta yi nasara a wannan fafatawa ta gaggauta magancewa
Wasu mutane sanye da kayan sarki a Nijar sun yi awon gaba da Moussa Tchangari jagoran kungiyar fafutuka ta Alternative, bayan da suka kutsa gidansa a daren jiya Talata jim kadan bayan dawowarsa daga Abuja kamar yadda wani na hannun damarsa Kaka Touda Goni ya bayyana wa manema labarai
Yayin da tawagar mataimakin Firai Ministan Rasha ta kammala rangadin kasashen Sahel da Nijar a karshen mako, wasu ‘yan kasar sun bayyana fatan ganin talaka ya amfana da wannan hulda, a daidai lokacin da ake fuskantar tabarbarewar dangantaka da kasashen yammacin duniya.
Kasar Chadi ta ba da sanarwar kawo karshen yarjejeniyar ayyukan sojan da ta sabunta da Faransa a shekarar 2019. Gwamnatin Chadin ta ce ta dauki wannan matakin ne da nufin jaddada ‘yancin kanta shekaru 66 bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Jami’an hukumomin shige da fice ko Douane daga kasashen Afirka ta Yamma da ta Tsakiya sun fara gudanar da taro a birnin Yamai da nufin bitar halin da ake ciki a sha’anin shige da ficen kaya a kan iyakokinsu da neman hanyoyin magance wasu matsaloli.
A yayinda wa'adin cika shekara da ficewarsu daga kungiyar CEDEAO, ministocin cikin gidan Nijar, Mali da Burkina Faso sun amince da sabon samfarin fasfo da takardun kasa da za a fara amfani da su domin yin bulaguro a maimakon fasfon ECOWAS da ake amfani da shi a yanzu haka
EU ta janye jakadan na ta ne domin ta ji ta bakinsa bayan da gwamnatin Nijar ta zarge shi da saba ka'ida da saka son rai wajen kasafta wani tallafin jin kai na Euro milion 1.3 da kungiyar ta bayar domin agaza wa 'yan Nijar da ambaliyar ruwa ta shafa.
Shugabannin kungiyoyin kwadago da na jam’iyyun siyasa da jami’an fafutika masu yaki da akidar mulkin mallaka daga kasashen Afrika, Asia da na kudancin Amurka ne ke halartar wannan taro.
A wani abinda ke fayyace alamun baraka a tsakanin hukumomin Mali, fira ministan gwamnatin rikon kwaryar kasar, Dr Choguel Maiga ya caccaki shugaban rikon kwaryar kasar, Janar Assimi Goita da mukarrabansa.
Malaman makaranta a Jamhuriyar Nijar sun fara yajin aikin kwana biyu daga yau Litinin da nufin tada hukumomi daga barci a game da wasu dadaddun bukatun da suka ce an yi biris da su duk kuwa da cewa magana ce ta kyautata rayuwar malamai
Kungiyar Transparency International ta gargadi mahukuntan Jamhuriyar Nijar da su soke yarjejeniyar ayyukan gina matatar da suka cimma da kamfanin Zimar na kasar Canada bayan da ta ce bincikenta ya gano cewa kamfanin Zimar na daga cikin irin kamfanonin da ke kewaye wa hanyoyin biyan haraji
Shugabanin kabilun karkarar Filingue dake jihar Tilabery a Nijar sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a yayin taron sulhun da hukumar wanzar da zaman lafiya ta shirya da nufin kawo karshen zaman doya da manja da aka fuskanta tsakanin al’umomin yanki mai fama da aika-aikar ‘yan bindiga da barayi.
Kasar Morocco ta gina wa Jamhuriyar Nijar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da injinan man dizel kyauta a yankin babban birnin Yamai.
Masu fufutukar kare muhalli sun yi tattaki a yau zuwa birnin Yamai na Nijar da nufin nuna rashin jin dadi game da abin da suka kira jan kafar da ake fuskanta wajen tilasta wa kasashen da ke gurbata muhalli biyan diyya sakamakon illolin da suke haddasawa al'umomi da muhalli a kasashe masu tasowa
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum a Jamhuriyar Nijar sun fara bayyana matsayinsu dangane da zaben Amurka na ranar Talata 5 ga watan Nuwamba bayan da aka ayyana dan takarar jam’iyyar Republican Donald Trump a matsayin wanda ya yi nasara a fafatawarsa da Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat.
A yayinda a yau Amurkawa ke halartar rumfunan zabe domin kada kuri’ar raba gardama a tsakanin Kamala Harris da Donald Trump a fafatawar neman shugabanci, masu bin diddigin siyasar kasa da kasa sun fara zayyana wasu daga cikin muhimman ayyukan da ya kamata sabuwar gwamnatin ta maida hankali kansu
Gwamnatin mulkin sojan kasar Jamhuriyar Nijar ta cimma wata yarjejeniyar kafa wata sabuwar matatar mai da kamfanin Zimar na Canada da nufin samar da wadatar man fetur da iskar gas a kasar da na kasuwanci.
A sanarwar da suka fitar kungiyoyin, a karkashin jagorancin Issoufou Sidibe, sun fara ne da nuna gamsuwa kan wasu muhimman matakan da suka ce hukumomin mulkin sojan Nijar sun dauka daga lokacin da suka karbi madafar iko.
A makon da ya gabata an ji yadda masu bukata ta musamman suka jajirce akan aiyukan bunkasa damben zamani na guragu a kasar Ghana.
Domin Kari