Kawo yanzu ma’aikatar ilimi ba ta bayyana matsayinta dangane da wannan yajin aiki da kungiyoyin ke ikirarin ya yi tasiri a kan sha’anin karatu a illahirin jihohin kasar ba.
Halin rashin tabbas din da aka shiga a game da maganar shigar da malaman kwantiragi a sahun ma’aikatan dindindin na daga cikin matsalolin da suka sa gamayyar Dynamique da Convergence kiran yajin aikin na Litinin 18 da Talata 19 ga watan Nuwamba da nufin tunatar da gwamnati bukatun malaman makaranta inji sakataren kungiyar malamai ta SYNACEB Sherif Issoufou.
Jami’ar kula da hulda da ‘yan jarida a ofishin ministan ilimi Hadiza Issa da Muryar Amurka ta tuntuba ta waya domin jin martanin hukumomi a kan wannan yajin aiki ba ta daga kiran ba sannan muka tuntubi matemakin magatakardan ofishin ministan Abdou Elhadji Idi shi ma bai amsa kira ba bai kuma amsa sakon text da aka aike masa ba.
Wannan shine karon farko da malaman makaranta ke kaurace wa aiki tun bayan juyin mlkin 26 ga watan Yulin bara koda yake a wani bangaren a jiya wasu kungiyoyin malaman sun yi kira ga magoya bayansu cewa kada su shiga yajin aikin da suke ganin abu ne da babu hujjar yinsa.
Tuni kungiyar uwayen dalibai APEE ta fara jan hankulan bangarorin a kan bukatar sulhu ta la’akari da yadda takaddamar malamai da hukumomi ka iya maida hannun agogo baya a harkokin karatun ‘yayan talakawa.
Gamayyar ta Dynamique da Convergence da suka ce kofofinsu na bude domin sulhu da gwamnati sun kudiri aniyar ci gaba da gwagwarmaya a kan maganar hakkokin malaman makaranta muddin basu ji wata amsa mai gamsarwa ba.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna