Hakan na faruwa a wani lokacin da Rasha ke kara kusantar kasashen Afirka kamar yadda a ranar Alhamis ma’aikatar tsaron Nijar ta ce ta karbi tallafin makamai daga hukumomin Moscow.
Mininistan harakokin wajen Chadi Abderaman Koulamallah ya bayyana a wannan sanarwa a ranar Alhamis din cewa gwamnatin Chadi ta dauki matakin dake kawo karshen yarjejeniyar ayyukan tsaro a tsakanin kasar da Faransa.
Sannan ta ce matakin ya biyo bayan dogon nazari a game da wannan yarjejeniya da kasashen biyu suka sabinta a ranar 5 ga watan Satumban 2019.
Ganin yadda matakin ke zuwa a washegarin ziyarar ministan harakokin wajen Faransa Jean Noel Barrot a N’djamena, manazarta na fassara abin a matsayin bazata.
Gwamnatin Chadi ta ce shekaru 66 bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka lokaci ya yi da za ta jaddada wannan ‘yanci a zahiri ta kuma sake tantance abokan huldarta a muhimman fannoni wadanda kuma ke daidai da bukatun kasar. Hakan ba ya nufin an zo karshen huldart a da Faransa kwata-kwata, wannan sabon matsayin na shugaba Mahamat Deby abu ne da ke janyo ayar tambaya.
Wannan al’amari da za a iya kiransa sabon babi a huldar Chadi da uwar gijiyarta wato Faransa abu ne da ke bayyana a wanil okacin da abokiyar hamayyar Faransar wato Russia ke kara samun shiga a yankin Sahel, wanda ko a jiya Alhamis kafar talbijan mallakar gwamnatin Nijar ta gwada wasu kayayyakin da ma’aikatar tsaron kasar ta karba a matsayin tallafin da Moscow ta aike don karfafa matakan yaki da ta’addanci.
Faransa da ke fuskantar koma baya a fannin diflomasiya a ‘yan shekarun nan msamman a tsakaninta da kasashen da ta yiwa mulkin mallaka na shan suka sakamakon girke sojoji a irin wadannan kasashe ciki har da Senegal.
Shugaban kasar Bassirou Diomaye Faye a hirarsa da wasu jaridun Faransar a jiya Alhamis ya kafe kan bakansa a batun kare ‘yancin kan Senegal abin da yake ganin ba zai cika ba muddin Faransa na ci gaba da girke dakarunta.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna