Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fatan Wasu Mutanen Nijar Kan Zaben Shugaban Amurka


Wasu Amurkawa Suna Kada Kuri’a Ranar Zaben Ranar 5 Ga Watan Nuwamba, 2024
Wasu Amurkawa Suna Kada Kuri’a Ranar Zaben Ranar 5 Ga Watan Nuwamba, 2024

A yayinda a yau Amurkawa ke halartar rumfunan zabe domin kada kuri’ar raba gardama a tsakanin Kamala Harris da Donald Trump a fafatawar neman shugabanci, masu bin diddigin siyasar kasa da kasa sun fara zayyana wasu daga cikin muhimman ayyukan da ya kamata sabuwar gwamnatin ta maida hankali kansu

A ciki da wajen kasar Amurka a bisa la'akari da yanayin tafiyar siyasar duniya a yau dai kasashen gabashi na ta yunkurin kwace shugabancin al’amuran duniya daga hannun takwarorinsu na yammaci ne.

Mahimmancin wannan zabe na 5 ga watan Nuwamba a wajen Amurkawa ya fice a misalta a bisa yadda akidar Dimokradiya ta zama wani bangare na rayuwar yau da kullum a kasar da ake yi wa kallon jagorar kasashen duniya.

Dalili kenan ‘yan kasar na ciki da waje ke halartar rumfunan zabe da nufin morar ‘yancin kada kuri’a, kamar Djbril Karfe wani Ba’amurke amma ‘dan asalin jamhuriyar Nijar.

A nan gida Afrika ma jama’a a kasashe daban-daban na bin diddigin wannan zabe sakamakon tasirinsa a kan huldar Amurka da nahiyar da yanzu ake ganin ta farka daga barci.

Masani kan huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye na fatan ganin sabuwar gwamnatin da za ta dare karaga bayan wannan zabe ta dauki matakin yayyafa ruwa kan wutar rikice-rikicen da duniya ke fama da su a yau, a kuma wani lokacin da hamayyar neman rike ragamar al’amuran duniya ke kara zafafa a tsakanin kasashen yankin Gabas da na Yammacin duniya.

Yanayin rayuwar al’umma na daga cikin mahimman fannonin da Amurka ke bai wa fifiko a huldarta da kasashen Afrika. A ra’ayin Malama Halima Lilou ‘yar fafutikar kare hakkin mata da yara ya zama wajibi wanda ya lashe zabe Republican ko Democrat a karfafa matakai a wannan fanni.

Ganin irin ce-ce-ku-cen da aka fuskanta a yayin yakin neman zabe da yadda muhawara kan wannan fafatawa ta yi zafin da ba a taba ganin irinta ba a tarihin siyasar kasar ta Amurka, kwararru na cewa yunkurin hada kan Amurkawa ya zama dole ga duk wanda zai yi nasara a wannan zabe.

Abin lura a wannan karon zaben na Amurka bai dauki hankulan jama’ar Nijar ba kamar yadda aka saba gani a yayin zabubukan da suka gabata lamarin da za a iya dangantawa da hatsaniyar da aka fuskanta a tsakanin gwamnatocin kasashen biyu a washe garin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Daidaikun mutanen da ke bayyana ra’ayi kan wannan zabe na dari-dari dangane da yadda sakamakon ka iya kasancewa, a bisa lura da abubuwan da suka wakana a fafatawar Trump da Hilary a 2016 inda kuri’un wakilai suka yi galaba kan kuri’un talakkawan kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Fatan Wasu Mutanen Nijar Kan Zaben Amurka Na 5 Ga Watan Nuwamban 2024.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG