Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Cimma Sabuwar Yarjejeniyar Gina Matatar Mai Da Canada


Aikin Gina Matatar Mai
Aikin Gina Matatar Mai

Gwamnatin mulkin sojan kasar Jamhuriyar Nijar ta cimma wata yarjejeniyar kafa wata sabuwar matatar mai da kamfanin Zimar na Canada da nufin samar da wadatar man fetur da iskar gas a kasar da na kasuwanci.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin jama’a da masu kare muhalli sun gargadi hukumomi akan bukatar daukan matakan rigakafin kauce wa gurbata muhalli da na murkushe yunkurin cin hanci ta yadda talaka zai mori kudaden shigar da za a samu ta hanyar wannan matata da za ta ringa tace ganguna 100,000 a kowace rana.

A karkashin wannan yarjejeniya gwamnatin Nijar da kamfanin Zimar Canada sun kudiri aniyar gina wannan matata bisa sharuddan daukan nauyin da suka hada da kaddamarwa tafiyar da ayyukanta, kulawa da abubuwan da ke da nasaba da gyare-gyare da a dai gefe dakin binciken kimiya.

Ministan tsaron kasa Janar Salifou Mody a madadin Firaiminista da jagoran tawagar Zimar Dr. Richar J. Moerman ne suka saka hannu kan wannan yarjejeniya a bisa gamsuwa da kwarewar kamfanin na Canada.

Janar Mody ya ce gina wannan matata a Dosso wani kudiri ne da zai bada damar cimma burin da aka sa gaba sannan wata dama ce ta daban da ta zo wa wannan kasa.

Wannan hulda ta musamman da kamfanin Zimar wani bangare ne na yunkurin bunkasa masana’antu masu dorewa da kuma samar da ayyukan yi da sauran damammaki ga ‘yan kasarmu. Sannan hanya ce da za ta bada damar samun makamashin da ake sarrafawa a gida.

Masu fafutikar kare hakkin jama’a a fannin ma’adinan karkashin kasa sun yaba da wannan yarjejeniya da suka ce hanya ce za ta samar da ci gaban kasa, sai dai sun gargadi hukumomi a kan maganar mutunta hakkokin jama’a da ayyukan ginin matatar zai raba da gonakinsu da sauran filaye.

Kafa kamfanoni da masana’antu musamman irin wadanda ke ayyukan hakowa ko sarrafa ma’adanan karkashin kasa abu ne da aka yi amannar cewa ya na tattare da illoli, dalili kenan masu rajin kare muhalli suka fara kiraye-kirayen ganin an dauki matakan riga kafin da zasu taimaka a kaucewa fadawa irin wannan matsala.

A cewar Ministan tsaro mai a madadin Firai ministan, gwamnatin Nijar na la’akari da dukkan wasu batutuwan da suka shafi muhalli kafin kulla makamantan wannan yarjejeniya sannan ya jaddada cewa sabuwar matatar za ta yi ayyukanta a karkashin tsarin bai wa ‘yan kasa da kamfanonin cikin gida fifiko a yayin daukan ma’aikata ko bada kwangiloli.

Jamhuriyar Nijar wacce ta fara hakar danyen mai daga rijiyoyin Agadem na jihar Diffa a shekarar 2011 a karkashin yarjejeniyarta da kamfanin CNPC na China kan tace ganguna 20,000 a kowace rana a matatar SORAZ dake Zinder yayinda a baya-bayan nan kasar da hadin guiwar CNPC suka soma fitar da ganguna 90,000 na danyen mai a kowace rana zuwa kasuwannin duniya ta hanyar bututun da ya ratsa kasar Benin.

Saurari cikakken rahato daga Souley Moumouni Barma:

Nijar Ta Cimma Wata Sabuwar Yarjejeniya Gina Matatar Mai Da Canada .MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG