Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: An Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Al'ummomin Filingue


Jihar Tilabery A Nijar
Jihar Tilabery A Nijar

Shugabanin kabilun karkarar Filingue dake jihar Tilabery a Nijar sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a yayin taron sulhun da hukumar wanzar da zaman lafiya ta shirya da nufin kawo karshen zaman doya da manja da aka fuskanta tsakanin al’umomin yanki mai fama da aika-aikar ‘yan bindiga da barayi.

Ganin yadda rigima ke kara tsananta a tsakanin al’ummomin karkarar Kourfey da suka hada da Hausawa, Bugaje da Fulani da Zabarmawa wadanda a ‘yan watannin nan suka yi ta kai wa juna hare-haren ramuwar gayya a yankin mai fama da ayyukan ‘yan ta’adda, ya sa hukumar wanzar da zaman lafiya ta HACP tattara hakiman garuruwan gundumomin Filingue da Abala don ganin an murkushe wannan matsala.

Hakiman sun kuma yafe wa juna a madadin jama’ar da suke shugabanta a yayin bikin da gwamnan jihar Tilabery ya jagoranta.

Karkarar Kourfey na daga cikin yankunan jihar Tilabery da ke fama da aika-aikar ‘yan ta’adda, lamarin da ake ganin ya taimaka wajen haddasa tsamin dangantaka a tsakanin kabilun da ke rayuwa wuri guda iyaye da kakanni.

Domin jaddada kyakkyawar aniyar mutunta alkawuran da suka dauka hakiman daya-bayan-daya sun yi rantsuwa a kan Alkur’ani mai tsarki a bainar jama’a.

Mukaddashin sarkin Filingue Adamou Idrissa Marafa ya yaba da halin kokari na bangarori a zaman da ya bada damar yin sulhu a hukunce na ganin abin a matsayin matakin nasara ga yunkurin maido da zaman lafiya.

Shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya Janar Amadou Didili dake jawabi a karshen wannan zama ya kudiri aniyar bin diddigin wannan yarjejeniya.

Ya ce ‘’ina sanarwa kuma ina jaddada aniyar cewa zan raka dukkan ayyukan da za a gudanar a karkashin kwamitin bin diddigi da aka kafa.

Tallafin HACP na nan tafe ga wanda hukumar za ta bayar domin mutanen da ambaliyar ruwan bana ta yi wa barna a gundumomin Abala da Filingue. Haka kuma HACP za ta taimaka a ayyukan fadakar da jama’a game da dokar hukunta laifukan da aka aikata a yanar gizo’’.

Karkarar Filingue mai makwaftaka da kasar Mali na fama da hare-haren ta’addanci da na barayin dabobi lamarin da ya sa al’ummomin yankin bullo da tsarin kare kai daga irin wannan ta’asa, abinda ya rikide zuwa fadace-fadace irin na ramuwar gayya a tsakanin jama’a duk da matakan da hukumomi ke dauka don tabbatar da tsaro.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

An Cimma Yarjejeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Al'ummomin Filingue Na Jihar Tilabery A Nijar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG