An ayyana cewa tashar za ta samar da mégawatt 18 a wani bangare ne na yunkurin rage dogaro da wutar da ake samu daga Najeriya.
Sai dai masana na bada shawara kan bukatar amfani da hasken rana ko iska ko kuma makamashin nukiliya domin samar da wadattacen lantarki.
Matsalolin da suka biyo bayan matakin katse wutar lantarkin da Najeriya ta dauka kan jamhuriyar Nijar a wani bangare na takunkuman CEDEAO masu nasaba da juyin mulkin 26 ga watan Yulin bara ya sa hukumomin Nijar shiga yunkurin neman hanyoyin da za su bai wa kasar damar dogara da kai wajen samar da wutar lantarki.
Yankin Yamai mai yawan jama’a kusan miliyan 1.5 na daga cikin yankunan da ke amfana da wutar da ake samarwa daga Najeriya.
Babban magatakardan kamfanin wutar lantarki NIGELEC Seybou Boubacar na cewa ‘’kafin abubuwan da suka wakana a ranar 26 ga watan Yuli mégawatts 100 ake samu daga Najeriya domin amfanin jihohin Dosso, Yamai da Tilabery to amma daga lokacin gobarar da aka fuskanta a tashar birnin Kebbi mégawatts 40 kacal ake samar wa Nijar.
Dukkan wutar da jama'a ke amfani da ita daga nan cikin gida ne ake samarwa.’’
Wannan ya sa hukumomin kasar suka shiga yunkurin karfafa matakai ta hanyar tuntubar kasashe aminnai. Morocco nan take ta amsa kira inda ta aiko da wasu ma'aikata da injinan wuta kimanin 9 a matsayin tallafi.
Malama Fati Abarchi shugabar kamfanin wuta na kasa NIGELEC.‘’Tace kwararrun ma'aikata 35 ne aka turo daga Morocco wadanda suka hada gwiwa da takwarorinsu 'yan Nijar domin girka wannan tasha mai karfin mégawatts 18.
Wadannan kayayyaki an ratsa da su ta Mauritania, Mali da Burkina Faso tare da rakiyar dakarun wadannan kasashe kafin a iso iyakar Nijar da su.” inda ta kara da cewa "wadanan kasashe sun cancanci yabo"
Kwararre kan sha'anin makamashi injiniya Rabiou Malan Issa ya yaba da fafutikar hukumomin na Nijar a wannan fanni.
Sai dai kuma a ra'ayinsa girman matsalar wutar lantarki a wannan zamani da bukatun jama’a ke ninkawa abu ne dake bukatar daukan kwararan matakai.
A shekarar 2017 gwamnatin Nijar ta gina tashar wutar lantarki da injin mai karfin megawatt 100 a kauyen Goro Banda dake kwaryar birnin Yamai sannan a 2023 kungiyar EU ta gina wata tasha mai aiki da hasken rana a kauyen na Gorou Banda don samar da megawatt 30.
A saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna