Jami’an tsaro na ‘yan sanda a jihar Zamfara sun ceto jarirai 19 da wasu 78 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da mata masu juna biyu da mata masu shayarwa da kananan yara.
Matasan sun nanata mara baya ga dokar nan ta zaben ‘yar tinke a fitar da gwani na jam’iyyu da shugaba Buhari ya ki sanyawa hannu, inda majalisa ta ce za ta duba lamarin a sabuwar shekarar nan.
Sakamokon wannan rashi da aka yi gammayar kungiyoyin ta sanar da jingine taronta da ta shirya yi a ranakun 5 da 6 ga wannan watan nan na Janairu.
Shekarar 2021 ta zo ta wuce, to amma kamar wadanda suka gabace ta, ta bar na ta tarihi, darussa da ababen koyi musamman a zukatan 'yan Najeriya.
Duk da tsarin dimokradiyya da a ke yi a Najeriya, masu sharhin sun ce ba a samun bambancin manufofin ‘yan siyasa a kowace jam’iyya ba, don tsarin jari hujja da ke nisanta talakawa da masu hannu da shuni ya kulla dangantaka tsakanin su.
Kawo yanzu dai hukumar ta DSS, ba ta bayyana dalilanta na kai wannan samame a ofishin na CISLAC ba.
‘Yan Najeriya sun mayar da martani game da kalaman Ministan Shari’ar kasar Abubakar Malami na cewa gwamnatin tarayya na amfani da kudaden da aka kwato a kasashen waje wajen gudanar da manyan ayyuka na ciyar da kasar gaba.
"Dokar za ta kuma kara ta’azzara kalubalen rashin tsaro, haka kuma ba ta wakilci ra’ayin akasarin ‘yan Najeriya ba"
'Yan bindiga sun yi garkuwa da Charles Mato, Sum Pyem din garin Gindri. Jami'an tsaron jihar sun ce an kaddamar da binciken gano inda yake da ceto shi.
Jami'an hukumar kashe gobara a birnin Abuja sun yi kira ga jama'a da su lura su kuma guji zuwa wurin da gobarar ke ci.
Yayin da gangar siyasa a Najeriya ke kadawa kuma lokacin zabubuka na dada zuwa kusa, Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana goyan bayan sa ga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo don tsayawa takarar zaben shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2023.
A daidai lokacin da al’umma a fadin duniya ke shirye-shiryen gudanar da bikin Krismeti da na shiga sabuwar shekara, ana cigaba da samun karuwan masu harbuwa da cutar covid 19 a Najeriya.
Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabon karamin ministan ayyuka da gidaje, Muazu Jaji Sambo, a fadar gwamnatin kasar dake birnin tarayya Abuja, jim kadan gabanin bude taron kwamitin tsaro na kasa da aka gudanar a yau juma’a
"Duk da irin matakan da gwamnatoci ke dauka na hana yawon barace-baracen almajirai, har yanzu wasu mutane na samun hanyoyin yawo da yara almajirai da sunan neman ilimi."
Kudaden da hukumar ta samu sun haura hasashen da aka yi na Naira tiriliyan 1.687, kuma an sami wadannan kudaden ne daga watan Junairu zuwa 19 ga watan Disamban shekarar nan ta 2021 mai ban kwana.
A daidai lokacin da yan’ Najeiriya da dama musamman daga yankin arewacin kasar ke korafe karafensu har da gudanar da zanga zanga akan tabarbarewar tsaro da ake fuskatanta a yankin wadansu kungiyoyi na neman a ba gwamnati lokaci.
Ƙungiyar marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ta turawa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya sakonnin halin da al'ummar Arewa suke ciki na taɓarɓarewar tsaro, musamman a ƴan kwanakin nan.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa zargin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Honarabul Ahmed Idris Wase ya yi na cewa akwai hadin kai tsakanin jami’an yan’sanda da yan’fashi a jihar ba shi da tushe balle makama
Gwamnatin Najeriya ta karawa jami’an ‘yan sanda albashi da kashi 20% da zai fara aiki daga watan Janairu na 2022.
Domin Kari