Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata A Gwada Ba Matasa Mulkin Najeriya A 2023 - Matasa A Zauren VOA


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Matasan sun nanata mara baya ga dokar nan ta zaben ‘yar tinke a fitar da gwani na jam’iyyu da shugaba Buhari ya ki sanyawa hannu, inda majalisa ta ce za ta duba lamarin a sabuwar shekarar nan.

Matasa a Najeriya sun ce lokaci ya yi da za a ba su damar jan ragamar mulkin kasar a zaben 2023 mai zuwa.

Wannan wata alama ce da wasu ke ganin matasa na Najeriya sun kosa da jiran cikakkiyar damar jagoranci, inda suka bukaci masu yawan shekaru su kauce su ba su fage don hawa madafun iko a 2023.

Matasan na magana ne a wajen daukar sabon shirin zauren matasa na VOA na farko a bana da a ka gabatar a ofishin Muryar Amurka na Abuja.

Ahmadu Adamu Giade da ke kan gaba a wannan ra’ayin, ya ce ba alamun wadanda su ka dade kan madafun iko na da ranar da za su ba da ‘yar dama ga matasa su hau karaga.

Shi ma matashi daga Yobe Yau Yakubu ya lissafa wasu daga shugabanni ne a Najeriya da su ka samu damar gudanar da mulki kuma su ka yi abin azo a gani a yayin da su ke da karancin shekaru.

Dattijuwa a taron Hajiya Mama Balaraba ta marawa matasan baya ta na mai cewa akwai bukatar yin garambawul ga masu jagoranci da ke son makalewa kan mulki har iya rayuwarsu.

Karshe dai matasan sun nanata mara baya ga dokar nan ta zaben ‘yar tinke a fitar da gwani na jam’iyyu da shugaba Buhari ya ki sanyawa hannu, inda majalisa ta ce za ta duba lamarin a sabuwar shekarar nan.

A wani labari da ke kama da wannan kuma wata matashiya 'yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a zaben 2023.

Khadijat ta kasance mai fafutukar 'yancin matasa da samar musu cigaba, kuma ta yi fice musamman a kafafen sada zumunta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Litinin, Khadijat ta fito fili ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Matashiyar ta kasance mace ta farko mai kamar maza, da ta bayyana fatan ganin ta gaji shugabancin Najeriya a babban zaben dake tafe.

XS
SM
MD
LG