Wadannan kalamai dai na Ministan ya fito ne yayin wata hira da aka yi da shi a wani gidan rediyo a jihar Kano, inda ya ce ana amfani da kudaden da aka kwato daga kasashen waje wadanda barayin gwamnati suka sace wajen aiwatar da manyan ayyuka a kasar da yaki da ayyukan ta’addanci da kuma gudanar da shirye-shiryen ayyukan jinkai ga al’ummar kasar.
Masanin al’amuran yau da kullum Sabo Iman Gashuwa ya bayyana cewa wannan batu bai zo wa 'yan Najeriya da mamaki ba saboda sun jima suna zargin gwamnati da kwato kudade daga hannun wadanda basu da gaskiya sannan wasu marasa gaskiyan suna sake kwashewa.
Ya ce kamar kudaden da aka kwato daga tsohon shugaban kasa Abacha har yanzu basu ga abinda aka yi da kudaden ba. Ya kara da cewa ya kamata shugaban kasa ya hada wani kwamiti da zai duba kudaden da kuma ayyukan da za a yi dasu don talakawa su gani a kasa kamar ta fannen ilmi, kiwon lafiya da sauran su.
Mai Magana da yawun gamayyar kungiyar Arewacin Najeriya Abdulaziz Sulaiman ya yi kari da cewa kamata yayi ‘yan kasa su san nawa aka karbo kuma da abinda za a yi da shi.
Duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta wadanda ake dangantawa da rashin kayayyakin aiki da jami’an tsaron ke fama da su, Ministan ya bayyana cewa cikin shekara daya na mulkin wannan gwamnati ta shugaba Buhari an samu gagarumar nasara ta hanyar yaki da ta’addanci batun da masanin tsaro a kasar Yahuza Ahmed Getso ya ce duk shaci-fadi ce da borin kunya.
‘Yan Najeriya da dama ba su gamsu da wannan batu na Ministan Shari’ar kasar Abubakar Malami ba na cewa an yi amfani da kudaden da aka kwato daga kadarorin da aka wawashe, musamman wadanda aka ajiye a kasashen waje ta hanyar da ta dace.
Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim: