Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna Ta Karyata Zargin Hada Baki Da 'Yan Fashi


 Yan' sandan Najeriya
Yan' sandan Najeriya

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa zargin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Honarabul Ahmed Idris Wase ya yi na cewa akwai hadin kai tsakanin jami’an yan’sanda da yan’fashi a jihar ba shi da tushe balle makama

Hakan ya fito ne cikin wata sanarwa dake dauke da sa hannu jami’in hulda da jama’a na rundunar (PPRO), ASP Muhammed Jalige da ke cewa:

“An jawo hankalin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna kan wata jarida da ta yi ta yawo a kafafen yada labarai, inda ta ce akwai hadin kai da kuma sausauci a bangaren ‘yan sanda a yakin da ake yi da ‘yan fashi a jihar Kaduna, batun da aka ce ya fito ne daga bakin mataimakin kakakin majalisar wakilai, Hon. Ahmed Idris Wase."

Sanarwar ta kuma kara da cewa “A cikin watanni goma sha daya da suka gabata, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kasance kan gaba wajen yaki da ‘yan fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a jihar.

Hakan ya kai ga kama mutane 305 da ake zargi da hannu a jerin hare-haren ‘yan bindiga da fashi da makami da garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja da sauran kananan hukumomin jihar ta Kaduna,”

Kazalika Sanarwar ta bayyana cewa an gurfanar da mutane 242 da ake zargi gaban kotuna daban-daban na jihar. Kana jami’an yan sandan sun yi nasarar kwato jimillar manyan bindigogi da makamai 161, da alburusai 2,924 a ayyukan yaki da masu aikata laifuka daban-daban.

“Haka kuma, an yi nasarar ceto mutane 168 da aka yi garkuwa da su tare da sake hada su da iyalansu,”

Don haka sanarwar ta ce babu wani lokaci da rundunar ta taimaka ko ta hada kai ko bada goyon bayanta ga aikata wanin mumunar laifi a jihar

A ranar Talata ne Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Idris Wase (APC, Filato), ya zargi wasu jami’an tsaro da hada-kai da ‘yan bindigan da ke ta’adi.

Dan majalisar ya bada misalan lokuta uku da ‘yan sanda suka saki mutanen da ake zargin ‘yan bindiga ne ko masu garkuwa da mutane ko ma ‘yan fashi.

A cewar Wase, akwai ‘yan sandan da suke kawowa gwamnati cikas wajen yakar miyagu, yace da irin wadannan jami’an tsaro ne ake cutar da yankin Arewa.

XS
SM
MD
LG