Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce kawo yanzu ta samar da kudaden shiga na Naira tiriliyan 2.3 a asusun tarayya a shekarar 2021.
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na hukumar Timi Bomodi ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da kuma kafafen yada labarai kan hanyoyin saukaka kasuwanci a jihar Legas.
Bomodi ya bayyana cewa kudaden da aka samu sun haura hasashen da aka yi na Naira tiriliyan 1.687, kuma an sami wadannan kudaden ne daga watan Junairu zuwa 19 ga watan Disamban shekarar nan ta 2021.
Ya ce duk kuwa da tarin kalubale da annobar Covid-19 ya zo da su a shekarar 2021, wanda ya yi mumunar tasiri ga rayuwar al’umma ta yau da kullum a fadin duniya, hukumar ta Kwastam ta yi gaggarumin nasara cikin ayukanta.
“Zan iya tabbatar maku da cewa mun samu sama da Naira tiriliyan 2.3, ma’ana mun samu abin da ya wuce harinmu na Naira tiriliyan N1.687 a shekarar 2021, kuma Mafi yawan kudin-shigan da hukumar ta samu sun fito ne daga tashar Apapa da Tin-Can Island” in ji kakakin.
A cewarsa, Hukumar kwastam tana mai da hankali kan mutunta yanayin aiki da ka'idoji da kuma koyi kan kasuwancin kasa-da-kasa.