Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba Elkana wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Gusau, ya ce an ceto mutanen ne daga dajin Shinkafi da Tsafe.
A cewar Elkana, mutum 68 da aka ceto daga dajin Shinkafi da aka yi garkuwa da su sama da watanni 3 sun hada da; Manya maza 33, yara maza 7, yara mata 3 da mata 25 ciki har da masu juna biyu da masu shayarwa.
Ya kara da cewa, an yi garkuwa da su ne daga Magarya, Maradun, Gusau na jihar Zamfara da Sabon Birni na jihar Sokoto.
CP Elkana ya ce, an kubutar da wasu mutum 29 da aka yi garkuwa da su daga karamar hukumar Tsafe, inda ya ce an yi garkuwa da su tsawon kwanaki 60 daga kauyukan Adarawa, Gana da Bayawuri a gundumar Rijiya ta karamar hukumar Gusau.
Sun hada da mata 25 ciki har da da mata masu juna biyu da masu shayarwa da kuma yara maza 4.
Ra’ayoyin Da Ku Ka Aiko Mana Kan Tambayar Da Muku A Wannan Mako
Ceton ya biyo bayan matsin lamba da aka samu sakamakon ci gaba da kai farmakin da sojoji suka kai a kusa da sansanin fitattun shugabanin ‘yan bindigan Bello Turji and Ado Aleru, a cewar CP Ayuba Elkana Sadi.
Elkana ya kara da cewa, za a bayyana wadanda aka ceto tare da mika su ga gwamnatin jihar domin ci gaba da hada su da iyalansu.
Da yake karbar mutanen da abin ya shafa a madadin gwamnatin jihar Zamfara, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, DIG Mamman Tsafe (rtd) ya yabawa jami’an tsaro kan kokarin da suke yi na dakile matsalolin tsaro a jihar.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen kawo karshen duk wani nau’in aikata miyagun laifuka a jihar, don haka ya bukaci jama’a da su goyi bayan yakar ‘yan fashin da ake yi
Saurari karin bayyani a cikin rahoton Sani Malumfashi: