Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, a jiya, ya bayyana cewa an kafa wata shari’a ta farko a kan mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar Abba Kyari kan zargin zamba da gwamnatin Amurka ta yi masa da ya shafi wani mutum mai damfarar yanar gizo, Hushpuppi.
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta mika takardar sanarwar fara shirin tsige mataimakin gwamnan jihar Mahadi Ali.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta kama mutane 96 da kamfanoni 123 da kuma 'yan kasuwan canji 33 da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta'addanci a kasar.
Majalisar Dattawan Najeriya ta shiga tsakani kan batun barazanar bore da daliban makarantun jami’oi daga yankin arewacin kasar suka yi.
Kasa da sa’oi 24 bayan sanarwar Hukumar kula da kafofin yada labarai ta NBC a Najeriya ta dakatar da shahararren shirin gidan radiyon VISION da talebijin na Farin wata mai suna ‘’Idon Mikiya’’ masu ruwa da tsaki, ciki har da mahukuntan gidan radiyon sun fara tofa albarkacin bakinsu.
Ana dai zargin Rochas da hada baki da wasu kamfanoni guda biyar da wani dan siyasa daga jam’iyyar APC mai suna Anyim Nyerere Chinenye da wawure kudaden gwamnati a cikin tuhume-tuhume 17 da hukumar ta EFCC ta shigar babbar kotun tarayya da ke Abuja a jiya Litinin
A can baya shugaba Buhari ya ki rattaba hannun amincewa da sabuwar dokar zaben da majalisar dokoki ta gabatar masa, saboda a ganinsa, ta saba wa tsarin dimokaradiyya da ya ba da dama da zabin hanyoyin tsayar da 'yan takara.
Kalubalen rashin kyawun yanayi ya dakatar da shugaba Buhari daga ziyartar jihar Zamfara daga Sokoto don jajantawa al’ummar jihar bisa yawan hare-hare ‘yan bindiga da kan yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi.
Najeriya na matsayin na 154 daga cikin jerin kasashe 180 da rahoton ya duba.
Salisu Mukhtari ya ce kasancewar yaron dan karamar hukumarsa ce, ya dau lauya don bin kadin yaron kuma zai yi tsayin daka sai an tabbatar da adalci.
A dai jihar ta Legas aka fara samun bullar cutar ta COVID-19 bayan da aka samu wani dan Italiya da ita.
Hedkwatar tsaron Najeriya DHQ ta ce ta halaka 'yan ta'adda 49 a karkashin ayyukan sojinta yayin da wasu 'yan ta'adda 863 da iyalansu sun mika makaman su a makonni biyu da suka gabata.
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Abdulsalam Abubakar ya bukaci gwamnatin Najeriya ta janye shirin kawar da dukan tallafin man fetur.
Hasashe ya yi nuni da cewa idan aka dore da wannan karin kudin makarantu da daliban ke kuka akai, akwai yiyuwar mata su fi yawa wajen fita daga makarantu
Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya da ake kira CNG ta yi barazanar daukar matakin kauracewa dukkan kasuwanci da Ibo ke yi a fadin yankin arewacin Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi 'gyara kayan ka' ga ‘yan jam’iyyar sa ta APC cewa in sun ki hada kai za su iya shan kaye a zaben 2023.
Daya daga mazauna kauyukan karamar hukumar Anka a jihar Zamfara, Murtala Waramu ya ce shi da sauran jama’a sun kirga gawa 52 da ‘yan bindiga su ka yi wa kisan gilla a wani mummunan farmaki da su ka kai.
Wasu ‘yan kasar na ganin wannan nadin na zuwa ne a kurarren lokaci kamar yadda Usman Ma’azu ke cewa.
Domin Kari