Daliban sun yi barazanar gudanar da boren ne, sakamakon karin sama da kashi 100 na kudin makarantun jami’o’in da sauran makarantun gaba da sakandare da ake biya, lamarin da ya tunzura daliban shirya gudanar da zanga-zanga a fadin kasar domin nuna adawarsu kan batun.
Wannan dai ya biyo bayan jan hankalin majalisar dattawan Najeriya da sashin dalibai na gamayyar kungiyoyin arewacin kasar su ka yi kan batun karin kudin makarantun jami’o, lamarin da a cewarsu ke zuwa a lokacin da bai dace ba, idan aka yi la’akari da yanayin matsin tattalin arziki da kuma tarin matsalolin rashin tsaro da kasar ke ciki.
A hirar shi da Muryar Amurka, Komrad jamilu Aliyu Charanci shugaban bangaren dalibai na gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya ya ce sun gana da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal kan batun kuma ya bada tabbacin cewa a matsayinsu za su yi dukan mai yiwuwa don ganin an shawo kan matsalar.
A nashi bayanin, Sanata Ahmad Babba Kaita, shugaban kwamitin kula da harkokin jami’oi da manyan makarantu a majalisar dattawan Najeriyar ya bayyana cewa, majalisar dattawa ta ji koke koken daliban kuma yana da muhimmaci a kalle su da idon basira domin lokaci ne da komai ya ta'azzara kuma ace za'a kara kudin makaranta.
Gwamnati ta yi alkawarin karin kashi 50 cikin 100 a kasafin kudinta na wannan shekara ga bangaren ilimi, sai dai masu kula da lamura na cewa, har yanzu da sauran tafiya idan aka kwatanta da kashi 15 zuwa 20 da kasafin hukumar kula da ilimi da al’adu na majalisar dinkin duniya UNESCO ta nemi kasashe su ringa kebewa a duk shekara ga bangaren, da Shugaba muhammadu buhari ya amince wajen tabbatar da Najeriya ta bi tsarin cimma wannan manufa,
Rahotanni na nuni da cewa, wannan kari na kudin makarantu na iya sanya daliban cikin tsaka mai wuya inda wasu kan iya barin karatu sakamakon rashin iya biyan sabon kudin.
Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta gaza biyan bukatun malaman jami’o’in musamman kan yarjejeniyar da suka cimma a baya.
Saurari rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja Najeriya